Tarihin Auren Saratu Daso, adadin Ɗiyan ta da Jikokin ta

Tauraruwar Masana’antar Kannywood mai suna Saratu Gidado ko Daso a taƙaice ta ba masoyanta dama a kundinta na dandalin Instagram inda tacce su mata duk tambayar da suke so zata basu amsa. Jarumar wadda ke yawan fitowa a matsayanin uwa a yawancin faifayen shirin Kannywood ta rubata haka ne a turance, tace “Ask me any question about myself now” ma’ana su mata tambaya gameda ita zata basu amsa inda ta samu sharhi kusan dari biyu da kusan hamsin(about 250 comments) gamida martanin da take maidowa. Mu ma mun mata tambaya amman har yanzu bata kai ga bada amsar tamayar tamu ba.

Saratu Gidado dai na ɗaya daga sanannun jaruman Kannywood wanda sunka ginata tun farkon farko. Ance Daso ta shafe wajen shekaru sha-takwas(18) tana fitowa a akwatunan kallonku. Ita malamar makarantace kuma tana yawan fitowa a matsayin uwa ko muguwa wanda ta sha amsar kyautukkan kambunan yabo domin su.

Tana ɗaya daga masu faɗa a ji a masana’antar kuma uwa ce ga dukkan jarumanta maza da mata saboda mutumcin dake tsakaninta da su tun can

Daso tayi aure wajen ukku a tarihin rayuwarta; na farko tun tana budurwa, na biyu bayan mutuwar aurenta na farko ta shiga harka Hausa film nan ma ta sake wani aure wanda bai daɗe ba ya mutu, na ukku shine auren mijin da take aure yanzu Alhaji Muhammad Lawal wani dan kasuwa. A cikin tambayar da aka mata tace tanada Diya su hudu(4) da Jikoki ashirin da bakwai (27). Allah shi masu albarka.

Wasu sun mata tambayar shin wai da gaske ita jakadiyar sarkin Kano ce?

Sai dai Daso bata amsa wadannan tambayoyi ba inda tacce abune wanda ya shafeta ita kadai za’a tambayeta.

Sannan wani ya tambayeta cewa mi yassa take fitowa a faifayen shirin kwaikwayo alhalin tana da aure?

Sai ta bashi amsar cewa ai a kowace sana’a da aiki akwai ma’aurata.

Madogara: Hutudole.com

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post