Gwamna Ganduje ya shirya, ya yo shiga irin ta Saraki

Yanzu dai maganar da mutane ke ta magana kanta itace batun ba wasu tsohhin Masarautu dake Jahar Kano cikakken iko daidai da na Masarautar Kano. Masarautun sun hada da Masarautar Gaya, Masarautar Bichi, Masarautar Karaye da Masarautar Rano. Tun bayyanar wannan hoton a yanar gizo magoya bayan Gwamna Umar Abdullahi Ganduje suke ta mai kirari da Sarki Rano, Sarkin Karaye, Sarkin Bichi, Sarkin Gaya, wasu kuma suna sukarshi bisa zancen cewa siyasace yake saboda Maimartaba Muhammadu Sanusi II bai bashi goyon baya ba lokacin zaben da ya gabata na wannan shekarar 2019.

Tun kwanakki biyu dai ake ta takaddama a majalissar Kano tsakanin Gwamnan Jahar ta Kano da Sarkin Kano inda Gwamnan ya darma damarar kacancana karfin Masarautar Kano zuwa gida biyar. Yayi ta shan sharhi da suka daga wasu Kanawa da wajen Kano, gameda wannan abun da yake anniyar yi ga masarautar mai dimbin tarihi, inda bangare guda kuma suke ganin kamar cigaba ne garesu musamman Masarautar Rano wadda sunka ce martabarsuce za’a dawo musu da ita ta shekaru dubu daya(1,000) a tarihance.

Tun bayan wannan dai mun samu cewa Gwamnan Jahar yana shiri da kulle-kullen tsige Maimartaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II wanda ya ci tura. Wannan shiri da ya bijiro da niyyar raunana shi ba yi bane. Allah yasa a yi mai kyau.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post