Hukumar EFCC ta yi babban kamu a Jahar Zamfara

Abun nema ya samu, yau Talata, 28 ga watan Mayu 2019, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wadda ake kiraya da (Economic and Financial Crimes
Commission, (EFCC)), reshen Sokoto, ta yi nasarar kame wani Dansiyasa da kudi takarda tsagwaronsu da kimaninsu ya kai Naira Miliyan Sattin (N60, 000, 000 (Sixty Million Naira) bayan an samu kwakwaran shaida danganeda almundahana da kudi da yake yi. Mai laifi Murtala Muhammad wanda kane ne ga Sakataren Gwamnatin Jahar Zamfara, Professor Abdullahi Shinkafi, ya shiga hannu ne a No.145 Igala Housing Estate, kallacin hanyar Byepass, Gusau, Jahar Zamfara.

Mahakumtan sun same shi da abubuwa tatattare dashi, Motar Toyota baka kirar Land Cruiser Prado Jeep mai lamba DKA 67
PX Kaduna shake da jikkuna gari yayi zafi 4 kowace na shake da Naira Miliyan Sha-biyar dubu-dubu, duka-duka Naira Miliyan sattin kenan. An samu bindiga tare dashi mai baki daya, da wata guda kirar gargajiya, harsasan bindiga da diyan bindiga sha-biyu (12).

Allah ya kyauta.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post