Hukumar Yan Sanda ta kama wani Malami da Laifin Luwadi da Ƙananan Yara – Sokoto

Bayan da kungiyoyin kare hakin biladama ke ta tsokaci dan dakile dadaddar al’adar nan ta bara da Malaman tsangaya ke sa kananan yara suna yi wanda daya ne daga kalubalen da Almajiranci ke fuskanta a wanga karni namu na 21 inda zaka ga yaro ko nono bai gama sha ba amman uwaye dan sakaci sai su turo Diyansu Malaman da Matayensu suna azabtarda su ana bautarda su – abunci sai wanda ba’a so ake basu. Kwanan nan Hukumar Yan Sanda reshen Jahar Sakkwato ta yi nasarar cabke wani Malamin Tsangaya a Arkilla Sakkwata da laifin aikata Luwadi da Almajiranshi su shidda (6).

Almajiran sun tona asiri cewa Malaminsu, Murtala Mode, ya sha masu fyade. Almajiran, masu shekaru tsakanin hudu (4) da sha-biyar (15), sun kara da cewa Malamin yana karbar kudi daga Abokan harkatai Yan Luwadi su tilasta masu yin kwanciya da su. Duk da cewa Malam Mode ya amshi laifin aikata aika-aikar saduwa da yara ukku a makarantar, yara shidda sun ce ya sadu da su. Mai laifin ya amshi laifin a jawabin da yayi, cewa Kaddara ce ta Allah.

Yayinda ake bada jawabi ga yan jarida ran Attanin, Kwamishanan Yan Sanda, Ibrahim Kaoje, ya ce ran 22 ga watan Mayu, wani lauya tareda Hukumar kasa ta kare hakkin biladama, Hamza
Liman, sun kai karar Mai laifin Hukumar Yan Sanda reshen Arkilla, daga nan aka kai ta zuwa ta Jaha.

Kwamishanan ya ce Almajiran akasarinsu daga makwabciya Jahar Zamfara
suke, karawa da cewa Mai laifin ya maida su bayin shi yana saduwa da su kamin Hukumar kare hakkin biladama su kawo masu agaji. Ya yi kira ga Uwayen yara su guji tura diyan su Makarantun Tsangaya nesa daga mazamnansu.

Madogarar DAILY NIGERIAN ta samu labarin cewa za’a rufe Makarantar Tsangayar yayinda Yan Sanda ke ta kokarin sake sada Almajiran da Uwayensu.

Yaran su shidda (6) yanzu suna karkashin kulawar Kungiyar kwato hakkin yara “Save The Child Initiative Sokoto”, inda Kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Nijeriya “Muslim Lawyers Association of
Nigeria”, MULAN, reshen Jahar Sakkwato take basu abunci.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post