Tarihin Margyayiya Hajiya Binta Kofar Soro wadda ta rigya mu gidan gaskiya

Jiya, 4 ga watan Mayu, Masana’antar Kannywood ta tsaya tsit yayinda ta ke jimamin mutuwar ɗaya daga fitattun jaruman ta mata, Hajiya Binta Kofar Soro, wadda ta rigya mu gidan gaskiya sanadiyyar ƴar gajerar rashin lafiya (an ce ciwon ƙafa) a gidan ta da ke cikin Birnin Kano. Abokan sana’ar ta sun sanarda rasuwar jarumar wanda an ka yi bisar ta a Birnin Kanon inda take gudanarda harkokin ta na kasuwanci da sana’ar Hausa film, amman asalin ta daga Jahar Katsina ta ke, mahaifarta kuma inda ta yi auren ta na farin.

Ɗiyan Margyayiya Hajiya Binta mata su guda ukku.

Kwanakki kaɗan bayan rasuwar ta margyayiyar ta yi wani bayani mai jan hankali a kundin ta na kafar sada zumunta inda ta ke neman gafarar mabiyan ta da abokan aikin ta na Kannywood ta na mai cewa “Ina neman gafarar ku. Allah ya gafarta muna gaba ɗaya.”

Jikokin Hajiya Binta Kofar Soro Ƴantawaye Maza.

Cikakken sunan ta shi ne Hajiya Binta Kofar Soro ko Hajiya Binta a taƙaice, kamar yanda abokan sana’ar ta a Kannywood ke yawan kiran ta. An haife ta ranar 24 ga wata Nuwamba a shekarar 1970 cikin garin Katsina. In kun ka lissafa kenan yau ta na da shekaru arba’in da tara (49) kenan. Ta yi karatun ta na allo da na boko duk a garin su Katsina kamin daga bisani ta yi auren ta na farko.

Margyayiya Hajiya Binta tareda Jikanyar ta.

Ta na da ɗiya tareda mijinta na farin kamin rabuwar su. Watannin baya ma ta yi shagalin bikin auren ɗaya daga cikin ɗiyan ta mata wanda mutane da dama sun ka yi dandazo dan taya ta murna.

Kamannin auren Ɗiyar ta inda ta ke tareda angon ta.

Fitattar jarumar ta na yawan fitowa a matsayin uwa a Faifayen shirin Kannywood, matsayin da ya wuce gaban wasan kwaikwayo, har a zahiri ƴan wasan su na ɗaukarbta tamkar uwar su saboda riƙon gaskiya, tausayi, shawarar da ta ke yawan ba su kamar ita ta haife su. Hajiya ƴar siyasa ce ta sahun gaba wadda ta ke gwagwarmayar ƙwato ma tallakawan yankin ta ƴancin su da a ke danne musu, ƴar kasuwa ce ita, sannan sai sana’ar da mun ka san ta da ita watau wasan kwaikwayo wadda a cikin ta ta yi fice wanda shi ke. Ta na ɗaukar matsayin uwa a faifayen shirin da ta ke fitowa, kwatamkwacin su Margyayiya Amina Garba, Jamila, Hajara Usman, Saratu Daso d.s.s

Margyayiya Hajiya Binta tareda Ɗiyar ta wadda su ke da kama guda.

Hajiya Binta ta na ɗaya daga cikin jerin ƴan wasan kwaikwayo ƴan asalin Jahar Katsina. Jarumar ta jima ta na haskaka akwatunan kallon ku. Kafar GobirMob.com na taya ɗaukacin Masana’antar Kannywood da Katsina jimamin rasuwar Hajiya Binta Kofa Soro. Mu na roƙon Allah ya gafarta ma ta, ya sa kwanciya hutu ce.

Ragowar Kamannan Jikokin Margyayiya Hajiya Binta Kofar Soro da Ɗiyan ta:
Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post