Masabkin Taron Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) wanda zai gudana a Birnin Yamai (Photos)

Kasar Jamhoriyar Nijar zata baƙunci taron tarayyar Afrika(African Union), AU a taƙaice. Tuni Shugaban kasar Muhammadou Issuhou yake ta faɗi tashi dan ganin ya ma bakin nashi masauki ƙayatacce wanda yake- abun a-zo-a-gani kuma da kamar kolliya ta biya kudin sabulu dan irin wannan ado da aka ma masaukin tarayyar Afrika ko a turai sai sanbarka. Hotunan masaukin nasu da wuraren gabatarda taro, wuraren shaƴatawarsu, makwancinsu sun ƙayatar ba shakka kuma sun nuna cewa kasar tana samun cigaba a hannun Shugaba Muhammadou Issuhou. Taron zai kankamane daga rana 4 ga watan Yuli zuwa 8 ga wata in Allah ya yarda.

Kungiyar tarayyar Afrika( African Union) a turance, an ƙandamarda ita ne a shekarar dubu biyu da biyu 2002 dan maye gurbin kungiyar OAU (Organisation of African Union) wadda aka fara kafawa a shekarar alif dari tara da sattin da ukku 1963. Kungiyar wadda keda mambobi hamsin da biyar (55) da sunka hada kasashen Nahiyar Afrika, tana da babban dakin taronta ne a Birnin Habasha, Adis Abeba kana kuma tana zaben wasu birane a fadin Afrika dan gudanarda tarukanta. A shekarar bana 2019 taron kungiyar zai gudana ne a Babban Birni Niamey na Kasar Jamhoriyar Nijar inda tuni ake ta shirye-shirye dan karɓar baƙuncin mahalarta taron.

Ga hotunan masaukin baki da sauransu:

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post