Matan Aure: I na kan durkusawa in ba Mijina abunci a baki, Jaruma Empire

Jaruma Hauwa Muhammed mai kayan mata wadda tayi kaurin suna wajen tsokaci ga yanda ake ta samu mutuwar aure a zamani ga namu, ta bayyana dalilin da yassa aurenta ya dore tsawon lokaci. Yar kasuwar mai kamfanin “Jaruma Empire” ta dora hoto a kafar sada zumunta inda ta durkusa gaban mijinta tana ba shi abunci a baki. Abun koyi ga matan aure dan tabbatarda kyakkyawar zamantakewa da su da mazajensu.

A turance ta sakaya hoton da cewa

“My name is Jaruma and I respect and honour my husband, I kneel to serve and feed him.” Wato ma’ana “Suna na Jaruma kuma ina daratta tareda karrama mijina. Na kan durkusa ma mijina dan ciyarda shi da biyayya gareshi.”

Kyawo ba shi ke sa aure ko soyayya dorewa ba, biyayya da mutumta juna ne kadai ke sawa. Shawara ga matan zamani.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post