Fulani Makyaya da Jami'an tsaron SARs sunyi bata kashi jiya a Anambra

Mutanen wani gari dake kusada babban birnin Jahar Anambra sun kwana da gajiya jiya da rana yayinda wasu Makiyaya sunka far masu da halbe-halben bindiga kamar ana yaki daga neman sulhu. Rahotannin dake zo muna sunce rikicin gonakkine ya shiga tsakanin yan Kabilar na Ibo da Fulanin wanda wannan kuma sanannen abune da ya zama ruwan dare a fadin Nijeriya; ba ma a Kudancin Nijeriya ba kadai. Duk inda makyayi da manomi sunka gama wuri to ba’a cika mai kyau ba. Yan garin sun nemi sa bakin Jami’an tsaro inda nan ma abun bai haifar da da mai ido ba.

Ukwulu dai garine dake karkashin karamar hukumar Dunukofia, Jahar Anambra, kuma akasarin mutanen garin manoma ne. Su kuma Fulanin dake zama dabra da kauyen garin ance sun jima suna gudanarda harkokinsu na kiwo wajen kamin wanga sabanin ya shiga tsakaninsu da yan garin.

Yanzu dai maganar da ake fadan da aka gwabza jiya, 4 ga watan Yuli da rana, an samu salwantar rayukka sanadiyarshi wasu kuma sun jikkata. Ance Makiyayan sun kashe Jami’an tsaron SARS mutum biyu inda su kuma Jami’an SARS din sunka aika Fulani biyar har lahira sanadiyar rikicin.

Wannan dai ya biyo bayan da Gwamnatin tarayya take shirin kafa ma Fulanin Makyaya (Ruga – Rural grazing area) a fadin kasar, wanda a cewarta zai kawo karshen yawan fadace-fadace da rikittan da ke shiga tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma a kasar. Shirin da ya samu kakkausan suka daga yan Nijeriya daga bangarorin Jahohin Ibo, Jahohin Yarabawa da wasu na Hausawa saboda irin wanga sakamakon da kan iya biyowa baya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post