Sakamakon Fyade An yanke ma Wata Yar Pakistan Mummunan Hukumci Gaban 'Yangidansu

Shin ka san adalci? Minene adalci? Shin adalci ne a hukumta wani a kan laifin wani? Labarin wani mummunan abu ne da ya faru a Ƙasar Pakistan, Ƙauyen Rajpur cikin garin Muzaffarabad da ke Masarautar Punjab, inda an ka yanke ma wata budurwa hukumcin fyaɗe gaban ƴan gidan su saboda a na zargin ɗan uwan ta da aikata laifin fyaɗe ga wata mata a garin na su.

Abun dai shi ne Umar wanda a ke zargin shi da yi ma ƴaruwar Ashfaq fyaɗe a ranar 16 ga watan Juli inda abun ya kai ga kai ƙara wajen manyan gari, take babban shugaban garin ya yanke hukumcin cewa za’a yi ma ɗiyar Umar mai kimanin shekaru 16 fyaɗe a gaban ƴan gidan su inda Ashfaq ne da kan shi zai aikata fyaɗen dan rama ma ƴaruwar shi.

Sai bayan yanke wannan ƙazamin hukumci da manyan gari sun ka kira da adalci dangin Umar wadanda sun ka ɗaukaka ƙara ga ƴan sanda dan bi ma ɗiyar su hakkin ta, hukumar yan sandar sun ka yi awon gaba da manyan garin su guda 30 haɗi da Umar da kuma Ashfaq tareda ɗaukar alkawarin tsaurara bincike da kuma kira ga Gwamnati dan a kara wayarda kan mutane kan cin mutumcin mata a duniya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post