Uwargidan Shugaba Buhari ta yi Yaji tsawon Watanni

Uwargidan Shugaba Buhari wato Aisha Muhammadu Buhari ta kai kimanin watanni biyu cib-cib yanzu ba ta Nijeriya abunda ya fara janyo ce-ce kuce a fadar Villa har wasu suke ganin ko yajine na aure ta yi tsawon lokacin, namu ra’ayi. Bayanan da muke samu daga majiya mabambanta na cewa uwargidan ta bar kasar ne a dalilin yin bore bisa yanda gwamnatin maigidanta ke gudanar da abubuwa a kasar. Haka kuma Daily Trust ta tattaro muna bayanin cewa tun dai da uwargidan Shugaban kasan ta tafi kasar Saudiya a farko wata Agusta dan yin aikin hajji har yanzu ba ta dawo ba.

Mahajjatan da sun ka tafi kasar Saudiya dan sauke farali daga nan Nijeriya sun jima da dawowa gida, amman sai dai wata majiya wadda ke da kusanci da Villa ta sanar damu cewa tun bayan kammala aikin hajjin uwargidan shugaban kasan ta wuce Birnim London.

“Mama (wato uwargidan shugaban kasa) tana Birnin London. Daga Saudiya ta wuce zuwa Birnin London,” kamar yanda wata majiyar ta fada muna. Da kuma an ka tambayi majiyar labarin dawowarta sai ta ce: “Ban sani ba, abunda kawai na sani shi ne tana Birnin London.” An fara lura da cewa lallai bata kasar kasancewar anata yin abubuwan da ya kamata a ganta a wurin amman shiru kake ji.

Bugu da kari, wakilin Daily Trust ya bada tabbacin cewa hatta bikin babbar sallah da Shugaban kasa yayi a Dauran Jahar Katsina, inda yayi ta karbar manya-manyan baki matar ta shi bata nan. Gani na karshe da aka yi ma Aisha Buhari shi ne a farkon watan Yuli da sun ka tarbi Jakadiyar Jamhoriyar Nijar a Nijeriya tare da maigidanta Shugaba Buhari a fadar Villa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post