Zakara ya ci Ɗankunnai Mai tsada ya sha yanka a Ƙasar Habasha

Zakara ya shiga hannu a Kasar Habasha bayan da ya hadiye dan kunnen zinare na wata mata yar kasuwa. Zakaran da yayi tsada ya sha wuka karshe dan ciro dan kunnen da ya hade, inda an ka yanke mai farashi mai tsoka dan kubutarda Dankunnen na matar.

An tilasta ma yar kasuwar sayen zakaran saboda ta tsira da dankunnen nata da zakaran ya hadiye.

Matar mai suna Hachaltu Bedira ta je cin kasuwar Woliso, a Jahar Oromia dodan saida kajinta a daidai lokacin da ake gab da fara bikin sabuwar shekarar kasar.

Amman ba ta tafi kasuwar da niyyar sayo zakara ba, kuma zakaran na wani dan kasuwa ne da shi ma ya zo cin kasuwar.

Sai dai an shiga rudani a lokacin da zakaran ya tsere daga hannun ubangidan shi tare da fizge dan kunnen zinaren na Hachaltu tare da hadiye shi nan take.

Dole ‘yan sanda sunka shiga batun, tare da cabke zakaran da ya tada husumar bayan da lamura sunka dagule.

Babban jami’in ‘yan sanda Tadesse Bedada ya shaida ma BBC cewa bayan dogon nazari sun gano za a iya warware matsalar ne kawai tsakanin ‘yan kasuwar biyu.

Daga karshe dole mis Hachaltu ta sayi zakaran dala 5, kwatankwacin Naira 1,790. Wanda hakan ya saba ma ainihin kudin da ake saida turkakken zakara kamarshi a kasuwar.

Mai zakaran ya amince da farashin dan rage asara, wanda hakan shi ne mafita ga matar saboda ta samu a yanka shi kana ta ciro dan kunnenta na zinare da zakaran ya hade.

Jami’in ya kara da cewa a lokacin da suke tsare da zakaran, sun lura yana ta raba idanu, saboda gano abubuwa masu launin zinare dan ya hadiye.
BBChausa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post