Jarabawa: Ƴan Makarantar Jami'ar Danfodiyo (UDUSOK) sun jawo cece-kuce

Ko kun ga wani hoto na daliban Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato (UDUSOK) da ya ɗauki hankulan mutane kwanan ga a kafofin sada zumunta, tsakanin jiya da shekaranjiya. Wani ya bayyana hoton ƴan makarantar a kafar Twitter karƙashin wutar fitilar hasken rana da dare wanda ɗayan daliban ya ɗora suna karatun su gabanin fara jarabawa dan raha, amman abun da ya yaɗu a gizo sai ya yi juyi ya koma suka ga Gwamnatin Jahar Sakkwato da Tarayyar Nijeriya, cewa sun kasa samarda isassar wutar lantarki ga jami’o’i na tarayya (Federal Universities). Mutane da dama sun fito fili sun yi sharhi gameda hoton kamar haka:

Dalibi mai ƙwazo ba zai taɓa karatun cikin wanga yanayi ba. Gungun daliban UDUSOK ne da basu ɗauki karatun su da muhimmancin bane.

Wani kuma ya yi martani tareda kira ga Gwamnati

Dalibi na iya ɗaukar karatu kowane lokaci, a kowane yanayi. Abunda ake bukata shine kawai Gwamnati ta samarda isassar wutar lantarki ga mazamnin yan makarantun jami’o’i da sauran abubuwan more rayuwa.

Fassarar sharhukkan.

Hoton dai ba wani abun batsanci an ka yi cikin shi ba, ba’a aikata wata ta’asa a ciki ko wani abun ashsha ba, illa ƴan makarantar ne an ka haska a ciki suna ɗaukar karatun su cikin yanayi wanda sun ka ga ya dace dasu dan shirin shiga ɗakunan jarabawa kamar yanda an ka saba.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post