Kamannan Malamar da ke waƙiltar Nijar a Gasar Karatun Alkur'ani ta Duniya a Dubai (Photos)

Kamar yanda mun ka samu daga sashen NijarHausa24 a Facebook ta hannun Ashirou Kornaka, waɗanda sun ka baza hotunan yarinyar mai shekaru ashirin da ukku (23) tana gudanarda nata karatun Alƙur’ani– zagaye na huɗu a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Birnin Dubai. Ɗalibar mai suna Shafa’atou Issoufou Mouhmmadou ta ƙayatarda mutane sosai, inda ta sha ruwan addu’o’i da fata nagari daga mutanen kasar Nijar da makwabta, cewa Allah yasa ta ciwo ma Kasa Nijar matsayi na farko. Gasar musabakar karatun Alkƙur’anin ta duniya na gudana ne a halin yanzu a Birnin Dubai. Sannan kuma wasu masharhanta suna kyautata zaton ko diyar Shugaba Mouhammadou Issouhou ce, ganin sunayen mahaifinta ya zo daya da shi Shugabana Jamhoriyar Nijar din.

GobirMob na muku fatan alheri da nasara…

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post