Labarin wani Ɗan Jahar Katsina da ya kafa Tarihi a Jami'ar ABU Zaria

Ɗan Makarantar nan da sunan shi ya yi tashe ƴan kwanakkin ga a yanar gizo, Dr. Sale Murtala Dandashire, ya bayyana cewa ya na daga sirrukan nasarorin shi jajircewa, himma da dagewa da maida hankali ga karatun shi. Sannan ya shawarci dukkan ƴan makaranta da su ɗauki wannan a matsayin makami a fafutukar su ta neman sani a duk makarantun da sun ka tsinci kan su. Dr. Dandashire ɗan garin Ketare a karamar hukumar Kankara da ke cikin Jahar Katsina, ya kafa tarihi a Jami’ar ABU Zaria inda ya lashe kambunan yabo guda goma sha-ukku (13) a bikin gama karatun shi da makarantar karatun likitanci (ABU Medical School) ta gudanar na shekarar bana 2019. Yaron ya zama gwarzo a darussa kamar haka:
1. Best in Physiology
2. Best in Surgery
3. Best in Haematology
4. Best in Anatomy
5. Best in Histopathology
6. Best in Project (Community
Medicine)
7. Best in Biochemistry
8. Best in Chemical Pathology
9. Best in Pathology
10, Best in Med. Micro
11. Best in Commed
12. Best in Pharmacology
13. Best Graduating Student

Labarin gwarzon ɗan makarantar ya ɗauki hankulan mutane matuƙa a kafofin sada zumunta; Twitter da Facebook, ganin cewa gurbin karatun likitanci (Medicine course) abu ne ba mai sauƙi ba. Ƙarawa da ƙarau, mun samu labarin cewa wanga ba shi ba ne karo na farko da Jami’ar ABU Zaria ta ke yaye ƴan makaranta likitoci da sun ka yi zarra a kasar, shekarar bara ma 2018, sun yaye wata yarinya macce mai suna Dr. Aisha Humairah Abaji ƴar asalin Jahar Nasarawa da ta samu kambunan yabo guda tara (9). Bana an samu namiji wanda ya doke ta da kambu guda huɗu (4).

Tsangayar karatun likitanci ta Jami’ar ABU, watau Ahmadu Bello Univesity Medical School, Zaria ta ce nasarar Dr Dandashire ba ta shi ba ce shi kadai, ta ƙasa ce baki ɗaya, musamman yankin Arewa da ma Gwamnatin Jahar Katsina.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post