Tsoho Tandja Mamadou na nan da ran shi bai Mutu ba

Labari ya bazu shekaran jiya Assabar a kafofin sada zumunta; Whatsapp da Facebook cewa Tsohon Shugaban Kasar Jamhoriyar Nijar, Shugaba Mamadou Tandja ya rasu, wannan labarin ya biyo baya ne yayinda mutan kasar ke jimamin kisan kyashin da mayaƙan Abzinawa sun ka ma Sojojin ƙasar wajen su kimanin tamanin (71) bakin iyakar Nijar da Mali,satin da ya gabata. Ana ciki kururuwar, kwatsam sai mun ka samu labarin cewa ba da gaske bane, yana nan da ran shi bai mutu ba. Ƙarawa da ƙarau kafofin yaɗa labarai na duniya irin su BBC Hausa, RFI Hausa da VOA Hausa basu fito sun ka tabbata mutuwar ba. Ga hotunan shi nan tareda iyalinshi, matarshi da ɗiyanshi maza da mata:

Mun samu labarin ne daga wata majiya mai tushe wadda ta musanta mutuwar ta shi a dandalin Whatsapp. Malamar take bayyana cewa wata shirya-shirya ce ake so a ƙulla dan ɓadda labarin sojojin da yan ta’addar ISWAP sun ka kashe kwanan baya,ganin abun yayi munin gaske.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post