Asirin Masu Garkuwa da Mutane ya tonu a Ƙasar Libya

Tun bayan kifewar Tsohuwar Gwamnatin Muammar Ghaddafi a shekarar 2011, mutanen Jamhoriyar Larabawa, wato Libya, sun shiga wani matsi na halin rayuwa abun ashsha, dukiyoyi da dama sun salwanta, gine-gine da abubuwan more rayuwa abun kwatamce sun zama tarihi sai abunda ba’a rasa ba, sakamakon yaƙin da ƙungiyar NATO ta Amurka ta jagoranta a ƙasar dan ganin bayan shugaban mai kishi. Ba ƴan ƙasar kaɗai juyin mulkin ya takura ma ba, hatta ƴan cirani, saboda makaman da ƴan tawaye sun ka mallaka wajen kifarda tsohuwar gwamnatin suna amfani dasu wajen tada zamne tsaye a ƙasar– inda wasu ke gama kai da ɓata-garin ƴan cirani suna garkuwa da mutane dan su samu kuɗi. A baya sai ka ji ance wata hukuma a Ƙasar Libya ta kama mutane ana neman miliyoyin kuɗaɗe kafin a sako su. A gida sai a saida gonakki da gidaje a aika ko kuma a bar mutum ya fuskanci hukumcin da bai yi tsammani ba; kisan gilla ko ƴan bindiga su saida mutane a matsayin bayi. Kun ga yanda Libya ta koma bayan Gaddhafi!

Labari ya fita jiya a kafofin sada zumunta daga bakin ƴan cirani ƴan kasar Nijar dake zama Libya cewa asirin masu aikata waɗannan muyagun ayukkan ya fara tonuwa; sun ce hukuma ta kama wasu daga cikinsu, inda ake kan neman wasu. Ga hotunansu nan ƙasa. Mutunen guda da kuke gani, kamar yanda ya bayyana, kubcewa yayi daga hannun matasa tun kafin a hannanta shi a hannun jami’an tsaro. Dan haka yayi kira ga sauran dangi dake zama wajajen da su ankara ko an samu a kama shi.

Wanda ya watsa labarin a kafar Whatsapp ya ƙara da cewa Gwamnatin Nijar ta turo Jirgin sama na ƙasa dan maida ƴan ƙasarta gida– waɗanda abun ya rutsa dasu. Ya ce kuma waɗanda keda hannu cikin wannan ƙazamin aiki duk dukiyoyin da sun ka mallaka gida Nijar Gwamnati zata ƙwace su…

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post