Kano: Almajirai sun shiga Azuzuwan Tsangaya na Zamani

Sarkin Kano yayi kira ga Gwamnati da masu hannu da shuni kan hana tabi’ar nan ta ” bara ” cikin almajiranci da yara ƙanana da manya ke yi da sunan almajiranci ko karatun allo; tsarin karatu wanda mutanen yankin sun ka jima da shi shekaru aru-aru tun gabanin zuwan turawan mulkin mallaka. Maganar ta shi dai ta samu goyon baya sosai ga mutane, inda wasu kuma suke goyon bayan a daƙile almajirancin ma kwata-kwata saɓanin ra’ayin Sarki, saboda su a ganinsu shine yake haifarda ta’addanci a ƙasar da sauran matsaloli na rayuwa ga matasan Arewacin Nijeriya da kewaye.

Gwamnan Kano da ake ganin basu ga-maciji da Sarkin Kano shine ya shiga sahun gaba wajen tabbatarda ƙudurin na Maimartaba Sanusi Lamido Sanusi wanda yayi kira kan gyaran fuska ga halayen almajirai da almajiranci. Gwamnan Nasarawa shima mun samu labarin cewa ya hana bara a Jahar shi sakamakon kiraye-kirayen na mutane.

Yanzu dai maganar da ake an fara sanya almajirai azuzuwan zamani na “Tsangaya Schools” waɗanda Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya fara ginawa a faɗin Arewacin Nijeriya a shekarar 2009, ɗaya daga shirinsu na na seven (7) points agenda da Tranformation agenda.

A saƙon da Ali Nuhu ya ɗora kwanakkin ga a wata kafar sada zumunta, ya jinjina ma Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan namijin ƙoƙarin da yayi na hana bara tareda sanya yaran azuzuwan zamani dan su samu ilimin addini da na boko baki daƴa. Ya sakaya waɗanga hotunan tareda saƙon jijinar da addu’a ga Ganduje.
Ga ainahin rubutun na shi wanda yayi cikin harshen Ingilishi inda yake cewa:

May Allah reward you @govumarganduje for this giant stride, ameen.

Reposted from @gandujiyya_online Almajiri’s system of education this is (TSANGAYA SCHOOL) Thanks Baba Ganduje.
#gandujiyya_online
#almajiri
#almajirisystem

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post