Shin ka san Tarihin Ranar Masoya ta Duniya, Valentines?

Valentines day dai rana ce wadda masoya ke rarraba ma junansu kyaututukka dan nuna ƙauna da kuma ranar shagalin Kirista ta duniya a kowane zagayowar ranar 14 ga watan Fabrairu. An dai samo asalin sunan Valentine ne daga wani limamin kirista dake Rum mai suna Saint Valentine wanda yayi limancin cocin katolika tun karni na ukku (AD), wato bayan barin duniyar Annabi Isah Almasihu, wanda ya mutu daidai ranar ta 14 ga Fabrairu. Sannan tarihi ya bada cewa asalin ranar Valentine ta samo asaline a zamanin Sarkin yaki Claudis II na Ƙasar Rum. An yi zamanin da ya haramta ma sojojin shi yin aure dan kada su susuce wajen yaƙi, wanda hakan tasa wani mai suna Valentine yaga hakan a matsayin rashin adalci har ta kai shi ga shirya auren wasu masoya biyu a asirce wanda daga ƙarshe ya jawo ma kanshi shiga kurkuku ƙarshe an ka yanke ma shi hukumcin kisa. Ta hakan ne lokacin da yake gidan kaso kafin a kasheshi sai ya kamu da son wata ɗiyar mai kula da gidan yari har ya rubuta mata wata wasika mai taken “Kyautar Valentine” zuwa gareki. Wannan itace kyauta ta farko a matsayin kyautar Valentine da masoyi ya taɓa ba masoyiyarshi a tarihi.

Bayan gwagwarmayar turawan mulkin mallaka kuma sun ka baza al’adar ko’ina a fadin duniya a matsayin ranar soyayya ta musamman ga samari da ƴanmata– masoya juna, hatta ma’aurata aure ba’a bar su baya ba wajen gudanarda bikin Valentine.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post