Babban Dalilin Maida FCE Sabon Birni zuwa Gida Madi, Tangaza Sokoto

Yanzu zaman da ake ciki mutanen Yankin Sokoto-ta-gabas dake Arewa maso yammacin Nijeriya, sun shiga ruɗani gamida zaman takaici na abubuwa guda ukku (3), cikin ƴan watanni ukku; Na ɗaya, sakamakon Annobar Coronavirus, Hare-haren da Ƴan Ta’addan Fulani ke kaiwa ƙauyukka ba ji ba gani, sai cikon na ukku sauya zaman Kwalejin Ilimi wadda Majalissar Waƙilai ta ƙasa ta yarje a yankin a Shekarar 2018 “Federal College of Education Sabon Birni”, wadda Hukumomi yanzu sun ka maida a wani gari wanda ake kira Gidan Madi dake Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jahar Sokoto. Mun samu tabbacin cewa za’a maida makarantar ne can sakamakon ta’addancin da ya addabi yankin na Gobir, bayan tattancewar Jami’an Hukumar NCCE.

Bayan labari ya bayyana cewa za’a sauya ma makarantar mazamni, mutanen yankin sun yo ca a kafar Facebook dan su isarda kokensu ga Shugabannisu( Senator Ibrahim Abdullahi Gobir dss) da Gwamnatin Jaha wadda itace alhaki ya rataya ga wuyanta na ganin ta share musu kukansu. An samu diddigin labarin ne daga ɗayan yaran Senator Aliyu Magatakarda Wamako, wanda ke waƙiltar yankin da za’a maida ginin makarantar.

Tamabaya: Idan saboda ta’addanci ne za’a gusarda makarantar zuwa wani yanki to kenan ana nufin Gwamnati bata wani shiri na shawo kanshi a Sokoto.

#Savesokotoeastfrombanditry

#Savegobirfrombanditry

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post