Dubun Ƴan Bindigar Sokoto ta gabas ta fara cika

Yayinda Jami’an tsaro sun ka yi kunnen uwar shaggu da hare-haren ta’addancin dake addabar wasu ƙauyukka a Jahar Sokoto, Arewa maso yammacin Nijeriya, mutane ƙauyukka yanzu sun fara ɗaukar matakan kare kansu ƴan kwana kwananga. Yanzu matasa da majiya ƙarfi sun fara tashi suna kare ƙauyukkansu daga ƴan bindigar ba dare ba rana. Kwanan baya a Garin Kurawa dake ƙarama hukumar Sabon Birni, matasa sun yi sa’ar kama mutum guda da ya kamo wani bawan Allah da niyyar garkuwa dashi. Take sun ka mai dukan tsiya kafin su hannata shi ga Yan sanda; inda su kuma sun ka miƙama ƴan ta’addan shi bayan sun yi gargaɗin kawo musu hari. Jiya 21 ga watan Mayu, a Garin Garki an kama wasu ɓarayi su biyu da bindigogi. Sun zo cikin gari dan su gyara tayar motonsu da ta sace, shikenan sai matasan dake rangadin anguwa sun ka tunkaresu, inda sun ka gano bindigogi dake cikin buhun dake tareda su. Nan ma sun yanke musu hukumcin da ya dace inda sun ka ɗirka musu kashin tsiya.

Tun kafin shiga watan azumi ƴan ta’adda suke ta kai farmaki a wasu ƙananan hukumomi dake cikin Jahar; Sabon Birnin Gobir, Isah, Gada da Goronyo, inda alƙaluma sun ka bada cewar sun kai farmaki a garuruwa fiyeda ashirin (20), sun kashe mutane wajen ɗari ukku (300), sun ƙone dukiyoyi tareda sace shanu da kimaninsu zai kai dubu biyar da wani abu (5,000+). Mutanen da abun ya shafa sun sha koke-koke a kafofin sada zumunta har sun gaji, sun yi kiraye-kirayen, amman kawo yanzu babu labarin matakin da an ka ce an ɗauka. Abunda ya ƙara ba mutane tsoro da mamaki ma shine shekaranjiya Kwamishanan Tsaro na Sokoto da ya fito fili ya ƙaryata hare-haren da ƴan ta’addan Fulani suke kaiwa a ƙauyukkan jahar.

#StopBanditryinSokotoEast

#StopBanditryinGobir

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post