Federal Collage of Education Sabon Birni, Ina an ka kwana, Micece Mafita?

Tun bayan lokacin da Shugaban Hukumar kula da Makarantun Horarda Malamai wato National Commission for College of Education (NCCE), Mr Ameh Isaac, ya fitarda sanarwa cewa Gwamnatin tarayya ta yarda a gina sabbin makarantu (Federal Collages of Education) a faɗin Jahohin Nijeriya guda shidda Bauchi, Benue, Ebonyi, Osun, Edo da Sokoto, da basuda na tarayya. Gwamnatin ta ɗauki anniyar haka ne dan samarda gogaggun Malamai waɗanda zasu samu ƙwarewa ta musamman.  A Jahar Sokoto an yi sa’a ta faɗo inda ake buƙatarta – yankin Sokoto-ta-gabas, bayan gwagwarmayar da Maigirma Senator Ibrahim Abdullahi Gobir yayyi na ganin an ginata yankin da yake waƙilta dan a bisa ƙididdiga, tun kafuwar Jahar Sokoto a shekarar 1976 ba’a taɓa kawo wata jami’a ko makarantar gaba da sakandare yankin ba, dukkan jami’o’in Jahar suna Garin Sokoto da waɗanda ke kusa dashi. A Sokoto gari dakwai Jami’ar Usman Danfodiyo University Sokoto, Sokoto State Polytechnic, sai Sokoto State University wadda ke garin Wamakko dakeda nisan kilomita ashirin da ɗaya (21) daga Birnin Sokoto, duk cikin yankin Sokoto-ta-arewa. Tsohon Gwamnan Sokoto, Maigirma Senator Aliyu Magatakarda Wamako wanda ke waƙiltar yankin Sokoto-ta-arewa ya gabatarda takardar neman gina Federal Polytechnic Silame, wadda ita ma nisansu da Birnin bai wuce nisan kilomita hamshi (50) da ƙari ba . Gina manyan makarantu ko jami’o’i kusada Birni kamar Sokoto yanada nashi amfanin amman idan ana son Jaha ta cigaba dole sai ana rarrabawa zuwa sauran yankuna irinsu Sokoto-ta-gabas da Sokoto-ta-kudu.

Dalilin haka ne ma yassa Sardaunan Gobir, Senator mai waƙiltar Sokoto-ta-gabas ya ga ya dace a gina Federal College of Education Sabon Birni, ya yi ta kai komo a majalissar waƙilai mataki bayan mataki har sai da ta tabbata da alamar “Senate Bill No. 103: Federal college of education Sabon Birini, Sokoto (establishment etc) bill, 2018 (SB. 425)”.

Ginata a nan zai yi matuƙar rana ga Mutanen yankin, Jahar Sokoto, Tarayyar Nijeriya kai har ma da Maƙwabciyarta Nijar da suke da iyaka ta Sabon Birni International Border. Ƙaɗan daga amfanoninta ginata nan zasu haɗa da rage rashin aikin yi da matasan yankin da jaha ke fama dashi, samarda ƙwararrun malamai waɗanda jaha da ƙasa zasu yi tunƙaho dasu, samarda kuɗaɗen shiga; ga Gwamnatin tarayya, Gwamnatin Jaha da yankin shi kanshi, rage cunkoso matasa a manyan birane dan neman ilimi dss

Mun samu labarai da suke ta yawo a kafofin sada zumunta musamman a bangaren mutanen yankin na Sokoto-ta-gabas, cewa za’a ɗauke wannan Makaranta daga nan a maidata Sokoto-ta-kudu, a ƙaramar hukumar Tangaza, Garin Madi.

Mutanen yankin dake harkar yanar gizo da waɗanda basu yi sun fito sun bayyana ɓacin ransu ganin za’a ƙwace musu abunda jagoransu ya nemo musu – abunda sun ka daɗe suna muradi dan ganin yankin nasu Sokoto-ta-gabas shima ya cigaba ya bunkasa kamar sauran yankunan ƙasar.

Madogara mai tushe daga bakin Hukumar Ilimi ta Ƙasa (Federal Ministry of Education) da Hukumar Makarantun Kwalegin Horarda Malamai (NCCE) sun fito ƙarara sun ƙaryata zancen, cewa za’a gusarda Federal College of Education Jama’are zuwa wani wurin, amman ta ce zasu turo hukumomi ran 11 ga watan Mayu dan tantance wurarenda za’a gina makarantun guda shidda (6) kafin a soma aiki. Ta ce wancan labarin kitsa shi ne an ka yi dan tada zamne tsaye. In ko haka ne to ta tabbata ko jita-jitar gusarda Federal College of Education Sabon Birni zuwa Garin Madi ba gaskiya bane kamar yanda hukumomi sun ka tabbatar.

Mafita ɗaya ce; Mutanen yankin su cire bambancin siyasa da suke fama dashi da na ƙabilanci, su haɗa kanunsu dan ganin hakan ta tabbata saboda cigabansu ne baki ɗaya. Idan ta kama akwai inda ƴan bokon nasu zasu yi rana, da ace da gaske ne, zasu iya kai ƙara Kotun ƙoli ta kasa wato “Supreme court” kamar yanda Ƴan Garin Jama’are, Jahar Bauchi sun ka ɗauki anniyyar ƙalubalantar abun a nasu ɓangare. Yan kasuwar yankin su ma sunada rawarda zasu iya takawa dan ƙwatoma ƴan yankin nasu hakkinshi idan ta kama. Kai harma da wasu yan yankunan Jahar Sokoto da sun ka damu da cigaban yankin zasu iya haɗa ƙarfi da ƙarfe. Bissalam.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post