Gwamnatin Nijar ta shirya Yaƙi da Ƴan Ta'adda a Iyakar Sabon Birni da Gidan Rumji

Dakarun Sojojin Jamhoriyar Nijar sun bazu a dajin yankin Guidan Roumdji (Gidan Rumji), Maradi Niger, wanda keda iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birnin Gobir, Sokoto Nigeria, inda ƴan ta’addan Fulani suke ta kai hare-hare ba dare ba rana tun gabanin shiga watan azumin Ramadhan. Ƙasar ta jibje tankokin yaki su wajen ashirin (20) a Garin Tsululu dan yaƙar ƴan ta’addan dake kwararowa yankin ƙasarta. Masu ruwaya sun bada cewar ƴan ta’addan suna kwararowa dajin ne da zarar sun kai hare-harensu a ƙauyukkan yankin na Sakkwato ta gabas; sun abka ma garuruwa wajen ashirin tsakanin Sabon Birni da Isa: Garin Tarah, Tagirke, Bafarawa, Makuwana, Kalgo, Ga’itace, Zangon ga’itace, Kurawa, Takalmawa, Gangara, Lajinge, Gatawa, Garin idi, Attalawa, Garin Bature, Adamawa, Nadamawa, Mallamawa, Dangaida, Burkusuma, Dankura, Dantasakko, Gamji, Dama Katsallen Kade, Katsallen Tanko, Gyangyadi, Magira, Araga , Garin Mallam, Sangerawa d.s.s

Cikin ƴan kwanakki ƴan ta’addan Fulani sun kashe mutane ba adadi, sun ƙone dukiyoyinsu tareda garkuwa da mutane da sace bisashen su; wasu wajejen kasuwanninsu suke ƙonewa ba tsoron Allah kamar yanda ya bayyana a hotunan dake ƙasa. Maganar da ake yanzu yawancin garuruwn da abun ya shafa sun yi ƙaura Jamhoriyar Nijar dan samun mafaka.

Hare-haren ya kan kama ne tun bayan da Jami’an tsaro sun ka ƙwace makaman kariya da mutanen yankin sun ka tanada dan kare kansu, kuma ƙarawa da ƙarau an ka soke yan ƙato da gora (sa kai), biyo bayan zaman sulhu da an ka ce an yi a Garin Isa wanda bai taɓuka komi ba.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post