Yan Ta'addan Fulani sun kai hari wani Gari a Sokoto

Jiya daidai ƙarfe takwas na dare (8:00pm) bayan an sha ruwa, yan ta’addan Fulani waɗanda alƙaluma suke bada cewar maɓuyar su na cikin ƙaramar hukumar Isa, sun sake kai ma wani gari a Sakkwato hari, Tagirde wanda yake ƙarƙashin ƙaramar hukumar mulkin Sabon Birnin Gobir, a Jahar Sokoto. Yayin harin an samu kafofi sadarwa a kakkashe balle a tuntuɓi jami’an tsaro su kawo ma ƴan garin ɗauki, ta bakin masu ruwaya.

Tun farkon shiga juyin-yuyin halin annobar coronavirus da ake ciki a halin yanzu, ƴanta’adda sun kai ƙazamin hari a Garin Gangara, shima a cikin ƙaramar hukumar, wanda yayyi sanadiyar mutuwar mutane ashirin da biyu (22) tareda ƙona dukiyoyin su ba adadi.

Wannan na faruwa ne tun bayan zaman sulhun da an ka ce an yi a garin na Isa na kawo ƙarshe hare-haren Fulanin yanta’adda a yankin, a zaman sulhun nasu an samu halartar Sarakai na yankin Sakkwato ta gabas, Shugabannin ƙananan hukumomi da manya dake faɗa a ji, cikinsu harɗa Major Garba Moyi d.s.s

A zaman taron an yanke shawarar garuruwan da sun ka mallaki makaman kare kansu kamo daga bindigogi da makamantansu su aje. Bayan taron Sojoji da ƴansanda sun bi garuruwa suna ƙwace makamai daga hannun mutane. Kuma bayan ance anyi sulhun ne waɗanga abubuwan suke faruwa.

Kaico! da Jikokin Malam Usman Danfodio wanda ya yaƙi Sarakunan Hausa da manufar “Haraji haram”– tarihi ya bada a haka shima ya fara a wancan zamanin har ya yaudari Hausawa a ƙarni na sha-tara (19). A namu ƙiyasci sai muce tarihi ne yake so shi maimaita kanshi tsakanin Gobirawa da Fulani, ganin yanda ƴan’addan Fulani suke ta kaima garuruwan Gobirawa hari ba ƙaƙƙautawa. Hatta Zamfarawa, Katsinawa da Kabawa basu bari ba. Kuma ma wai cikin wanga watan azumin Ramadana da ake ciki yanzu. Anya dai Fulani imaninsu ya kai zucci? Ban ga alama ba.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post