Yanzu rayuwar mu ta Dogara ne da Taimakon Sojojin Nijar – Senator Gobir

Mutanen Jahar Sokoto, a yankin Sokoto-ta-gabas a halin yanzu sun dogara ne da taimakon da Sojojin Jamhoriyar Nijar ke kawo musu saboda juya bayan da sojojin Nijeriya sun ka musu tun bayan hare-haren da ƴan ta’addan Fulani ke kawo musu tun bayan bayyanar Annobar Coronavirus. A yayin zaman majalissa, Sanatan mai waƙiltar yankin ya shaida ma majalissa halin da mutanenshi ke ciki na taɓarɓarewar tsaro; Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir ya ce aƙalla mutum dubu biyar sunyi gudun hijira zuwa kasar Nijar dan neman mafaka saboda halin ko’in kula na dakarun Sojojin Nijeriya, maharan sun kashe mutane wajen ɗari ukku gamida sace dukiyoyi da kimaninta ya kai miliyoyin naira.

Senator Gobir dai ya sanar da hakan ne a zaman majalisar daya gudana a yau Talata 19 ga watan Mayu.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post