Sojojin Nijar sun sake fatattakar Ƴan Bindigar Sokoto, sun kashe sama da 120

Mutanen yankin Sokoto-ta-gabas da hare-haren ta’addanci ya hanasu rumtsawa tsawon watanni suna ga bayyana farin cikinsu yayinda Dakarun Sojin Nijar sun ka tanki shirin kakkaɓar ƴan ta’addan da suke neman kutsawa ƙasar tasu ta iyakar Gidan Rumji/Sabon Birni. Tun tsawon watanni fiyeda ukku ƴan ta’addar Fulani suke ta kai hare-hare a Jahohin Arewa-maso-yammacin Nijeriya; Zamfara, Katsina da Sokoto, inda suke ta kashe mutane ba ji ba gani, su kwashe musu dukiyoyinsu tareda yima mata da ƙananan yara fyaɗe.

Jiya da rana Sojojin Niger sun samu galaba kan wata tawagar Ƴan ta’adda waɗanda sun ka addabi yankin Gatawa, Gangara, Taturu da Dozai dake yankin Isa da Sabon Birnin Gobir a Jahar Sokoto. Sojojin sun karɓi babura sama da 50 sannan sun samu nasarar amsar manyan makamai daga hannun Ƴan bindigar. Wani Shugaban Ƴan ta’addan ne ya kira rundunan Sojojin Niger ta waya yayyi musu barazana cewa idan sun isa su zo su cinmusu sansaninsu. A gumurzun da sun ka yi dasu sun samu galabar kashe Yan ta’adda sama da ɗari da ashirin (120), sun jikkata sama da arba’in (40) sun tafi dasu Maradi dake kasar ta Jamhoriyar Nijar. Da kyau.

Mutanen yankin sun bayyana farin cikinsu a kafofin sada zumunta kan ƙoƙarin da Gwamnatin Nijar ɗin take yi na yaƙi da Ta’addancin zai iya shafar mutan ƙasarta idan bata ɗauki matakin gaggawa ba, misalida Boko haram da ya shafi Maiduguri/Diffa. Ga ta bakin wani ma’abocin Facebook kan labarin:

Masha’Allah! Sojojin Nijar sunyi nasarar kashe bandits da dama a dajin burkusuma daya daga cikin kauyukan sabon-birni jahar sokoto, dake iyaka da nijar din. sojojin sun tafi da babura hamsin na bandits dinda suka kashe, sun kuma wuce da bandits arba’in
wadanda basu kashe ba. Ya Ubangiji Allah ka cigaba da tona musu asiri. Allah kacigaba da ba sojojin nijar sa’a akansu. wadanda keda hannu ga wannan cin zarafin da akeyima bayin Allah, Allah kada kabasu kwanciyar hankali anan duniya, ita lahira kodama sun san sauran.

Labarai cikin hotuna:

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post