Yanda Sojojin Nijeriya sun ka tarwatsa Mafakar Ƴan Bindiga a Sabon Birni

Mutane da yawa na ganin laifin Gwamnatin Shugaba Buhari na kasa ɗaukar matakin gaggawa dan daƙile hare-haren ta’addancinda yake neman zama ruwan dare a illaharin yankin Arewa. Sakamakon matakin da an ka ɗauka yau Alhamis, 24 ga watan Yuni a dajin Sangerawa/Burkusuma, Sabon Birnin Gobir dake Jahar Sokoto, zamu iya cewa an samu ɗan sauyi, saɓanin a baya da wasu ke shirin maida harkar tsaro “Siyasa” da neman na “Tuwo”, wanda hakan ya ƙara rura farmakinda ƴan ta’addan ke kaiwa a yankin. Dakarun Sojin sama na Nijeriya sunyi ma dajin Sangerawa dana Burkusuma ruwan bamabamai, wadda nan ne mafakar ƴan bindiga a yankin, bayan ta dajin Goronyo, dajin Isa, dajin Gada da wasu. An ruwaito cewa an samu ceto bisashen mutane daga wajen.

Ga ta bakin wani ma’abocin kafar Facebook kan farmakin:

Mashallah, Yau misalin karfe 6:30 na safe Sojoji sun yi nasarar tarwatsa Mafakar Ƴan Ta’adda dake addabar yankin Sabon Birni Local Govt, Sokoto State inda sun ka tarwatsa dajin kuma an ka samu nasarar kamo bisashe tsakanin Shanu da Awaki da Tumaki da Rakumai da Jakuna daga wajensu. Ya Allah ka kara taimakon Sojojin Nijeriya, masu sa hannu kuma Allah ka toni Asirinsu. Ameen ya Rabbil Alamin.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post