Jami'an Tsaron Nijar sun yi gagarumin kamu a Iyakar Gidan Rumji/Sabon Birni (Photos)

Rundunar Jami’an tsaron Gendarma na garin Maradi sunyi gagarumin kamu ran 6 ga watan Yuli inda sun ka samu nasarar cabke wasu ƴan ta’adda biyu dauke da muggan makamai na yaki suna neman tsallakawa dasu Nijeriya. An samu bindigogi AK-47 guda 21, harsashai ƙwara 6,124, maƙuddan kuɗaɗen naira har ₦309,000 da babur guda ɗaya wanda suke samanshi yayin kutsen. Jami’an sun taresu suna zummar tsallakawada makaman ta iyakar Sabon Birnin Gobir wadda ke ƙarƙashin jahar Sokoto.


Jami’an Gendarma(kwatamkwacin Mobile Police) dai sunyi gangamin shelantama mutane nasarar ne yau Juma’a, 10 ga wata Yuli, inda sun ka gabatarda ƴan ta’addan da muggan makamanda suke ɗauke dasu ga Gwamnan Jahar Maradi Zakari Oumarou da sauran manya mutane masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Jamhoriyar Nijar.

Labarai cikin hotuna:

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post