Sarki Ali Nuhu ya yi Magana kan Matsalar Tsaro a Arewacin Nijeriya

Jarumin Masana’antar Kannywood wato Ali Nuhu ya hassala kan kisan da ƴan Boko Haram sun ka yi ma manoma 110 a Jahar Borno. Ya yi tsokaci kan taɓarɓarewar tsaro da ya addabi yankin Arewacin Nijeriya, inda ya caccaki hukumomin tsaron ƙasar bisa zargin gaza shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta a Jahohin Arewa-maso-yammaci da Arewa-ta-gabas.

Ali Nuhu ya ɗora saƙo a kundin shi na Facebook mai suna “Ali Nuhu Mohammed” inda yake cewa;

Wannan al’amari na rashin tsaro ya dade da wuce Misalin, hakika in har akwai hukumomin tsaro a kasar nan to sun tabbata marasa amfani.

Ya cigaba da cewa;

Saboda kullum maimakon al’amari nan ya yi baya sai gaba ya ke. Shin abin tambaya anan shi ne, al’umar kasar ne ba damu da kare rayukansu da dukiyoyin su ba ko kuma rashin sanin makamar aiki ne?’ ya tambaya.

A ranar Assabar ne, 28 ga Nuwamba an ka samu labaran dake cewa wasu da ake tunanin Mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonakkin shinkafa a Zabarmari, Jahar Borno, inda sun ka kashe fiye da mutane arba’in (40) ta hanyar yi musu yankan rago, labarin da ya harzuƙa Ƴan Nijeriya, suke ta tofin Allah tsine ga Gwamnatin Ƙasar Nijeriya, tareda sabunta kiran ganin an yi watsi da shugabannin Tsaro da nauyi ya rataya ga wuyan su na ganin an samu mafita. Yanzu maganar da ake adadin waɗanda sun ka kashe a ranar ya zarta ɗari (100).

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post