Taron Wankan Sarauta a Garin Kornaka, Maradi Niger (Photos)

Jiya, 28 ga watan Nuwamba an ka yi bikin wankan sarauta a Masarautar Kornaka, wadda ke cikin yankin Dakoro a Jahar Maradi Niger. Sarki Habou Koure Jakou shine ya hau karagar Masarautar bayan rasuwar Tsohon Sarki, Margyayi Muhammed Akola Jakou, ƙane ga Sanousi Jakou. Tun a ranar 13 ga watan Afrailu masu zaɓen sarki sun ka tabbatar da shi, inda ya tsaya takara da su Sanousi Jakou.

Mutane da dama sun samu halartar taron. Manyan baƙi a taron sun haɗa da manyan Sarakunan Niger biyu, Maimartaba Sarkin Agadas, Ummaru Alhaji Ibrahim Ummaru, sai Maimartaba Sarkin Gobir Abdou Bala Marafa, da dai sauransu.

Allah shi taya ka riƙo. Ameen.

Kamannai daga Taron Bikin a Kornaka
Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post