Allah ne kaɗai zai iya tsare Iyakar Nijar da Nijeriya ba Mutane ba – Shugaba Buhari

Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya faɗi wata magana wadda sai an yi bincike. A yayin ganawar su da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ya faɗi wannan maganar wadda ta sa mutane zullumi, ya ce “Allah ne kaɗai zai iya kare iyakar Nijeriya da Nijar yanda ya kamata…”

Ya bayyana hakan ne a Fadar Aso rock yayin da yake ganawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa,  Namadi Sambo wanda kuma shi ne Shugaban Tawagar ECOWAS kan zaɓe zuwa Jamhoriyar Nijar ɗin.

Shugaba Buhari ya ce daga Daura ya fito dan haka ya na da masaniya akan ƙasar Nijar, ya ce shugaban ta mai barin gado mutumin kirki ne kuma su na tuntuɓar juna akai-akai.

Ya bayyana cewa, dakwai iyakar Nijeriya da Nijar wadda fadin ta ya kai kilomita dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400) wadda kuma Allah ne kaɗai zai iya kare ta yanda ya kamata. Shugaban ya ce za su ba Nijar dukkan goyon bayan da ya kamata dan ganin an yi zabe cikin Nasara.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post