Dalilin Naɗin Aminu Alan Waƙa Ɗanburan Sarkin Gobir (Photos)

Masarautar Gobir ta Sabon Birni, Jahar Sokoto ta tabbatar da Mawakin Hausa Dr. Aminu Ladan Abubakar ko Aminu Ala ko kuce Alan Waƙa a matsayin Ɗanburan Sarkin Gobir. Sarkin Gobir Maimartaba Isah Muhammadu Bawa ya bashi sarautar ne saboda gudunmuwar da yake badawa ga Masarautar da Ƙaramar Hukumar baki ɗaya kamar yanda an ka bayyana. Aminu Ala a kullum yana yawan kirara dangantakar shi da Masarautar Gobir a cikin waƙen shi. Idan mun ka bincika zamu iya gane cewa shi kamakunnan Sarkin Gobir Gwamki ne, bisa ƙididdiga da zancen da yayyi a cikin wata waƙa ta shi inda yake cewa “Maradi tayi babban baƙo”, lokacin da ya kai ziyara Masarautar Tsibirin Gobir, bayan wannan sai a wata waƙa mai take “Shahara” nan ya bayyana tarihin rayuwar shi tun daga kakannin shi na wajen uba da na wajen uwa. Yayi karatun shi na addini da boko duk a cikin Jahar Kano, a cewar shi.

Aminu Ala a halin yanzu yana riƙe da sarautoci guda ukku (3) Sarkin Waƙar Sarkin Kano, Sarkin Waƙar Sarkin Dutse, sai ta yanzu da ta tabbata Ɗanburan Sarkin Gobir. Allah ya taya ka riƙon.

Ga Saƙon Takardar Naɗin Sarautar a Rubuce:

ASSALAMU ALAIKUM
TAKARDAR TABBATAR MAKA DA SARAUTAR
DANBURAN SARKIN GOBIR
Gaisuwa mai yawa da yarda, Bayan haka
Ni Maigirma Sarkin Gobir da Ƴanmajalisa ta na bada dama da a naɗa Alh. Dr. Aminu Ladan Abubakar a matsayin DANBURAN SARKIN GOBIR saboda cancantar shi da bada goyon baya ga wagga
Masarauta da kuma Gwamnatin mu. Da fatan zaka rike wannan Amana.

Kamannan Aminu Ala da Sakon
Kamannan Aminu Alan Waƙa yayinda yake amsar Saƙo daga Maigirma Sarkin GobirAinahin Takardar Sako

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post