Jami'an Tsaro sun kama wani Malami bisa laifin Garkuwa da Yarinya ƙarama a Nasarawa

Hukumar Tsaro Mai kula da kare Haƙƙin Ƴanƙasa wato “Nigeria Security and Civil Defence Corps” (NSCDC), reshen Jahar Nasarawa ta kama wani mutum ɗan shekara talatin da biyar (35) Malam Musa Salihu Osike bisa zargin shi da sace wata yarinya ƴar kimanin shekara goma sha-shidda (16), Fatima Salihu, Ƴar Ƙungiyar Agaji na Matasan Musulmi a Yankin Giza a Karamar Hukumar Keana dake cikin Jahar Nasarawa.

Malam Musa, wanda shi ne Jagoran Ƙungiyar Agaji a Ƙaramar Hukumar Keana shi ma ya fito ne daga wannan yankin na Bunkasa tare da Fatima, wanda ake zargin shine ke da alhakin ɓacewar ta ba zato ba tsammani.

Bincike ya nuna cewa Musa, wanda zai halarci bikin sanya sunan a Lafia ya bukaci rakkiyar Fatima, da ƙawar ta Faiza Musa da wasu mutane tara waɗanda dukkan su ɗiyan ƙungiyar su ne.

A wata sanarwa da Muhammed Surajo Idris, PRO na NSCDC a jahar ya ce bayan sa’a ɗaya a wurin bikin sanya sunan, wanda ake zargin, Musa, ya sake tura su Anguwar Nungu a Lafia, babban birnin jahar dan shaƙatawa.

“An ce ya maida su Giza cikin motar shi amman daga baya ya kira Fatima ta zo ta karɓi sabuwar wayar da ya sayo ma ta. An ruwaito cewa ta bar Giza zuwa Lafia kuma tun daga wannan lokacin ba a san inda take ba ”.

“Wanda ake zargin wanda ya ke cikin gudu tun bayan ɓacewar yarinyar an kama shi ta hanyar tattara bayanan sirri.

“Duk da haka, Kwamandan Jaha na Ƙungiyar Agaji ta farko Alhaji Hassan Abdullahi ya dakatar da shi sakamakon mummunan aikin da ya aikata” in ji shi.

Za a gurfanar da shi a gaban masharanta da zaran an kammala bincike, sanarwar ta ce.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post