Malamin Coci ya ɗirka ma Ƴan Mata 20 ciki, Ya ce an mishi Wahayi

Wani Malamin Coci ɗan shekara hamsin da ukku (53), Mr. Timothy Ngwu ya ɗirka ma mabiyan shi su guda ashirin (20) ciki inda ya bayyana cewa wahayi an ka mishi ya yi hakan. Maganar da ake ciki yanzu, Malamin ya na hannun Hukumar Ƴansanda a Jahar Enugu, kamar yanda mun ka samu ruwaya daga Hutudole.

Timothy Ngwu wanda ke jagorantar Cocin Vineyards dake cikin Birnin Enugu shi ne yayyi wannan aika-aikar. Kakakin Ƴansandan Jahar, Ebere Amariazu ya bayyana cewa an kai shi masharanta inda an ka tuhume shi da cin zarafin mata.

Matar shi ce da abun ya ishe ta ta je ta gaya ma hukuma. Sai dai Malamin ya ce babu wadda ya tilasta ma, kowace sai da mijin ta ya yarda sannan ya ɗirka mata cikin.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post