Ruwan Rahama na ɓuɓɓuga daidai Kushewar Bawa Jangwarzo – Alkalawa (Photos)

Tun watan da ya gabata mun ka samu labarin wasu ruwa da ke ɓuɓɓuga daga ƙasa a tsohon zaman Gobirawa, Birnin Alkalawa. Ruwan sun bayyana ne dabra da katangar Kushewar su Bawa Jangwarzo wadda ke cikin garin Alkalawa, Sabon Birni, Jahar Sokoto. Mutane na ta dandazo a wurin dan gane ma idanuwan su, masu fama da cututtuka na zuwa su ɗebo su sha ko sun samu warkewa, inda wasu kau ke zuwa dan neman tubarraki.

Kamar yanda mun ka samu labarin daga bakin abokin aikin mu BabaAbu Gobir da Lawali Kakale Gobir, sun tabbatar da cewa ruwan sun daɗe da ƙwafewa a wajen, akasarin ko an tona ba’a cika samun ruwa ba, in bayan Rijiyar Kushewar Bawa Jangwarzo da ke kawo ruwa lokaci-lokaci, amman wanga karo kawai sai an ka wayi gari ruwa su na ɓuɓɓugowa daga ƙasa gwanin ban sha’awa da mamaki.

Manoma da ke noma a wajen su ne sun ka gano bayyanar wannan ruwan sun ka shaida ma mutanen Alkalawa da kewaye. Ga kwatamce, wurin ba shi da wuyar ganewa, ya na da nisan mita biyar (5) daga Garin Alkalawa wanda ke bisa babbar hanyar mota ta Sabon Birnin Gobir/Sokoto.

Matafiya su na yawan kai ziyara Gidan Tarihi da Kaburburan Sarakunan Gobir da ke cikin yankin da abun ya abku.

Sarakunan Gobir waɗanda kaburburan su ke wajen sun haɗa da:
Sarkin Gobir Ummaru Ibrahim Akal II ko Bawa Jangwarzo

Sarki Gobir Nafata Dangude

Sarki Gobir Yakubu Babari

Sarki Gobir Yumfa Nafata

Makwancin Uwar Bawa Jangwarzo, Aminatu

Makwancin Limamin Bawa Jangwarzo, Uwargidan shi, da sauran na wasu. Duka-duka dai kaburburan da ke Kushewar sun kai wajen ashirin (20), gamida na ƴantawayen Bawa Jangwarzo, wanda ya fi kowane tsawo da girma. Mun tambayi ɗaya daga masu tsaron kushewar, ya shaida muna cewa ƴantawayen su goma sha-biyu (12) wajen yaƙi sun ka zam babu. Allah ya kai haske kaburburan su. Ameen.

Kamannai na Ziyarar mu a Gidan Tarihin Gobir da Kushewar Bawa Jangwarzo a Shekarar 2017:

Ni da abokin aiki BabaAbu Gobir

Rijiyar Kushewar wadda Matafiya ke shan ruwa daga cikin ta.

A baya Kabarin Ƴantawayen Bawa Jangwarzo, jeri na gaba kuma Jangwarzo, Yumfa, Nafata, Yakubu, d.s.s

Tsawon Katangar Kushewar da ƙofar shiga. Masiyarta na yawan kawo ziyara Gidan Tarihi da Kushewar Bawa Jangwarzo wadda ke cikin garin Alkalawa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post