Taron Naɗin Sarautar Aminu Alan Waƙa a Sabon Birnin Gobir (Photos)

Maigirma Sarkin Gobir Isah Janguna Muhammadu Bawa ya gabatarda taron naɗin Sarautar Ɗanburan Sarkin Gobir jiya 30 ga watan Disamba 2020 a fadar shi, inda ya naɗa Fitaccen Mawaƙin Hausa Aminu Ladan Abubakar, wanda an ka fi sani da Aminu Alan Waƙa. Madogarar Junaidu Sabon Birni ta ce Sarakunan Gobir da sun ka shaidi naɗin sun haɗa da Maimartaba Sarkin Kudun Gatawa Mustapha Abdulhamid Balarabe, Sarkin Yamman Gobir Mainasara Salihu, Tawagar Aminu Ala da dai sauran su.

Maigirma Ɗanburan Masarautar Gobir jika ne ga Sarkin Gobir Bawa Dan
Gwamki wanda yayyi zamani a Birnin Tsibirin Gobir. Shi kau ɗa ne ga Sarkin Gobir lbrahim Gwamki Dankurar Gado. Kakan Aminu Ala ya gadi Sarkin Gobir Salihu Dan Yakuba, shi kuma ya gadi Sarkin Gobir Muhammadu Yumfa, shi
kuma ya gadi Sarkin Gobir Aliyu
Nafata, shi kuma ya gadi Sarkin
Gobir Yakubu Dan Babari, shi kuma
ya gadi Sarkin Gobir Ummaru lbrahim Bawa Jangwarzo, shi kuma ya gadi Sarkin Gobir Abdullahi Dan Gude Dan Uban Ashshe, shi kuma ya gadi Sarkin Gobir lbrahim Babari, shi kuma ya yadi Sarkin Gobir Muhammadu Akal. Allah ya ja zamin Ɗanburan Gobir. Amin
Daga: Isma’il Gobir.

Kamannai daga Taron Naɗin Sarautar:

Sarakunan Gobir na Sabon Birni yayin Naɗin  Sarautar

Ɗanburan Gobir Aminu Ala tareda Tafidan Sarkin Yamman Gobir

Tafidan Sarkin Yamman Gobir tareda wani Basarake

Maigirma Sarkin Gobir Isah Muhammadu Bawa yayin Naɗin Sarautar

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post