Ƙungiyar HURIWA na zargin Gwamnatin Shugaba Buhari da Goyon Bayan Ta’addanci a Nijeriya

HURIWA ko “Human Rights Writers Association of Nigeria”, wata ƙungiya ce da ke ƙoƙarin kare haƙƙin Bil’adama a Nijeriya. A wani bincike da ta gudanar, Ƙungiyar ta ce afuwa da neman sulhu da Gwamnati ke yima Ƴanta’adda su ne ke ƙara ruruta wutar Ta’addanci a Arewacin Nijeriya, maimakon ta ɗauki matakan kawar da su. Ta bayyana cewa, Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ce ke da alhakin duk hare-haren da ake kaiwa na Ta’addanci da garkuwa da mutane dan neman Kuɗin Fansa, saboda ta kasa ɗaukar matakan shawo kan matsalolin tsaro a Ƙasar.

HURIWA ta bayyana cewa ƙokarin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na kyautatawa da tausayawa ga Ƴanta’adda su ne ke ƙara musu ƙarfin gwiwa kan abubuwanda su ke yi.

Kungiyar ta bayyana waɗanga bayanan ne a matsayin martani kan sata da kuma sakin Ƴan makarantar Kankara Katsina da Ƴanta’addam Fulani sun ka yi kwanakkin baya.

Shugaban ta, Emmanuel Onwubiko ne ya bayyana hakan inda yacce afuwa da tallafin da Gwamnati ke ba Tubabbun Ƴan Boko Haram ke ruruta wutar hare-hare a Arewa-maso-gabaccin Nijeriya.

A ɓangaren Ƴanta’addan Fulani kuma, zaman sulhun da Sarakunan Fulani ke yi da Ƴan bindiga a Arewa-maso-yammacin Nijeriya.

Duk waɗannan matakan da su ke ɗauka ba su taɓa haihuwar ɗa mai ido. Ɗanta’adda ba’a sulhu da shi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post