Yaji: A’isha Buhari ta kai Watanni Biyu ba ta Fadar Aso Rock

An ruwaito cewa yau watanni biyu (2) kenan Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Buhari ba ta Fadar Aso Rock, wanda wasu masharhanta ke kallo a matsayin yajin aure karo na biyu (2). Na farkon mutane sun ce ta yi shi ne sanadiyyar ƙarin aure da an ka ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ƴan watannin da sun ka gabata.

A asirce A’isha Buhari ta bar Nijeriya zuwa Dubai da sunan duba lafiyar jikin ta, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

A ƙarshe wani Hadimin Matar Shugaban Ƙasar, Kabiru Dodo ya tabbatar da faruwar hakan inda yacce ba kamar yanda ake yayatawa cewa wai ta bar Nijeriya ne saboda matsalar tsaro ba, ta je ne dan neman magani, kuma ba za ta daɗe ba za ta dawo.

Ya ƙara da cewa ya na magana da ita akai-akai.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post