Zaɓen Nijar: Madugun Ƴan Adawa ya yi Kira mai Muhimmanci

Da sanyin safiyar yau, 11 ga watan Disamba, Madugun Ƴan Adawa Malam Hama Amadou ya kira Taron Manema Labarai inda ya amsa wasu tambayoyi da sun ka shafi Siyasar Nijar, ya kuma yi magana kan hana mishi Takarar Shugaban Ƙasa wanda wata Babbar Kotu a Birnin Yamai ta yanke hukumci, saboda wasu Laifukka da tacce ya yi a baya.

Cikin tattamnawar Malamin ya yi kira ga Ƴan Jamiyyar shi da masu goyon bayan shi da su nuna Kishi Ƙasa a Ranar Zaɓe mai zuwa.

Ga Kalaman shi inda yake cewa:

“Na yarda Kotu tayi watsi da Takarar
Shugaban Ƙasa ta, ina kira ga dukkan Ƴan
Jamiyyar mu ta Lumana Africa da su fito
Ranar Zaɓe su nuna Kishin Ƙasa, su kawar da Mulkin Zalumci da ke gudana a Ƙasar Niger. Ɓangaren zaben Shugaban Ƙasa kuwa
zamu yi shela mu faɗa ma Ƴan Jam’iyyar mu wa zamu goya ma baya”.

Zaɓen Nijar dai na Shugaban Ƙasa a Jamhoriyar Niger na ta ƙara ƙaratowa, zai gudana ne nan da sati biyu, ranar 27 ga wanga wata muke ciki.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post