Zaɓen Nijar: Wutar Lantarki ta ƙone Mutum Biyar

Yayinda zaɓen Jamhoriyar Nijar na shekarar 2020 ke ƙara ƙaratowa, jam’iyun ƙasar a na su ɓangare na ta ƙara ƙaimi wajen yaƙin neman zaɓe dan ganin cewa sun tallata ƴantakarar su ta yanda zasu samu yawan ƙuri’u.

Ana cikin haka wani mummunan abu ya abku inda wasu samari su biyar (5) sun ka ƙone yayinda suke shirin gangamin yaƙin neman zaɓe. An ce sun hau turken wutar lantarkin ne zasu ɗora tutar jam’iyyar wani ɗan siyasa turken wutar lantarki mai ƙarfin gaske ya faɗo musu ya yi sanadiyyar mutuwar samari biyar. Kamar yanda “Damagaram Post” ta ruwaito, labarin ya faru ne a babban birnin ƙasar, Birnin Yamai. Allah ya kyauta, ya gafarce su. Ameen.

Mutane sun kewaye gawarwakin samarin su na jimami.

Zaɓen zai gudana ne cikin wanga wata, Disemba, ranar 27 gare shi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post