Ƴan Bindiga sun sake kai hari garin Teke da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Jahar Sokoto

Yanzu mu ke samun labari cewa Ƴan bindiga sun shiga garin Teke su na ta’addanci tun bayan labarin kamun da Sojojin Nijeriya sun ka musu ranar kasuwar garin, ran Lahadi, 24 ga watan Janairu. Fulani ƴan ta’addar sun kai harin ne mai yiwuwa da niyyar rayuwar gayya kamar yanda sun ka saba. Majiyar Lawali Kakale Gobir ta tabbatarda cewa Sojojin Nijeriya sun kai ɗauki dan kwantarda ramuwar.

Ga dai abunda ya wakana tsakanin Fulanin Ɓarayin shanu a kasuwar garin

Ranar Lahadi 24 ga watan Janairu 2021 ranar ce da kasuwar garin Teke ta ci, kasuwa ce da ta yi suna ga kasuwancin bisashe a yankin Ƙaramar Hukumar Mulkin Sabon Birni, Jahar sokoto. Ta na haɗa yan kasuwar bisashe har daga Zamfara, yankin Sabon Birnin Gobir da Isa, yankunan da barayin bisashe da kisan mutane ya zama ba dare ba rana, ana zargin barayin shanu da ke satar bisashe su na kawo wasu daga bisashen da su ke sata a kasuwar dan su saida ma ƴan kasuwa.

Wasu Fulani da an ka sace musu shanun su ne sun ka zo dubawa a kasuwar kuma sun ka ga wasu daga cikin shanun su a turakun saida bisashe a kasuwar. Fulanin da sun ka kawo shanum ana zargin barayin ne, su na maganar sai rikici ya tashi tsakanin su. Fulanin sun ka hargitsa kasuwar da faɗa, ƴan sa kai da sun ka zo tare da Fulanin da an ka sace ma bisashe sun ka shiga dan kawo ɗaukin. Ana cikin wannan faɗan sai Sojojin Nijeriya daga Ƙaramar Hukumar Mulkin Isa sun ka shiga kasuwar daidai lokacin da ake wannan fada, ana zaton sun hallaka adadi mai yawa na barayin.

Bayan asarar rayukka da ba’a san adadin su ba a wannan faɗan da kuma munanan raunukka, an kuma kama mutane da dama yayin faɗan, kuma lokacin da Sojojin Nijeriya sun ka shigo kasuwar sun kwashe komi da komi zuwa Ƙaramar Hukumar Mulkin Isa.

Iyakar ɗan abunda da na iya ƙwarmatowa ke nan. Allah ne masani. Ubangiji Allah ya yi muna maganin abunda ya fi ƙarfin mu. Ameen.

Madogara: Lawali Kakale Gobir

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post