Ƙarshe Sheikh Ahmad Gummi ya bayyana Dalilan shi na shiga Dajin Jere dan yi ma Fulani Makyaya Wa'azi

Neman bakin zaren Matsalar Tsaron da yankin Arewacin Nijeriya ya faɗa ya sa mutane da dama tunanin yanda za su bada ta su gudunmuwa dan ceto yankin daga halin da ya tsinci kan shi a cikin ƴan shekarun ga. Malaman addini ma ba a bar su baya ba, dan ko a ƴan kwanakkin ga wani malamin Addinin Islama a Nijeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa ƙaramcin ilimi na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin Arewacin Ƙasar.

A hirar da yayyi da BBC Hausa, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana manyan dalilan shi na shiga dazukka da ke da matuƙar haɗari na hare-haren ta’addancin Fulani a yankunan Arewa-maso-yamma. Malamin ya ɗarma damarar kawo sauyi, inda ya fara da shirya wa’azin karkara a matsugunnan Fulani Makyaya, a Jere Kaduna. Sannan kuma ya ba Gwamnati shawarori waɗanda za su taimaka sosai wajen shawo kan hare-haren ta’addanci a yankin.

A cewar shi dalilan guda biyu ne, “Su waɗannan bayin Allah makyaya da su ke zamne a daji su na buƙatar wanda zai koyar da su addini, dan taimaka musu su fita daga jahilcin da su ke ciki, dan ko ya zama wajibi ne ga duk wani ɗan adam ya san ubangiji kuma ya bauta mishi,” in ji Sheikh Gumi.

“Da zarar an koya musu addini to zai kange su daga wannan ɓanna da su ke yi” in ji Sheikh Gumi.

Da an ka tambaye shi ko halin da su ke ciki na da alaƙa da sakacin Malaman addini Musulumci sai ya ce, “To ai Malaman addini kamar Ɗansanda ne na Gwamnati sai an biya shi zai yi wannan aiki, wane ne zai shiga daji ba a biya shi ba?, haƙƙin Gwamnati ne ta tabbatar da ilimin waɗannan mutane”.

Malamin ya ce a baya ya taɓa irin wannan yunƙuri lokacin da ya je hukumar kula da koyarda makyaya, su na da tsari da komi a lokacin amman abun da sun ka rasa shi ne kuɗin da za su rinƙa ɗaukar Malamai da su kuma su na biyan su.

Ya ƙara da cewa masu wannan sace-sace su na da ubanningida da ke gefe, saboda a lokuta da dama waɗanda su ke kama mutanen bai fi ₦30,000 kacal ake ba su a kuɗaɗen fansar da ake amsa.

Gumi ya ce ba wata riba su ke samu ba dan haka idan an ka yi musu tayin natsuwa za su karɓa cikin gaggawa.

Ubangiji Allah ya biya malam. Ameen

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post