Dara ta ci gida: Daga Sulhu Ƴan Bindiga sun kashe junan su a Jahar Katsina

A Jahar Katsina wasu gungunan Ƴan Ta’adda biyu sun samun rashin jituwa tsakanin su a ƙauyen Illela da ke cikin Ƙaramar Hukumar Safana. Rashin jituwar ya yisanadiyyar mutuwar ƴan bindiga da dama, da yawa kuma sun jikkata. An tuntuɓi mai magana da yawan Hukumar Ƴan Sanda ta Jahar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ana cigaba da bincike.

Rashin jituwar ya samo asali ne tun ranar Alhamis da ta gabata tsakanin ƴan gungun su Mani Sarki da Dankarami.

Majiya ta ce Sarki wanda yanzu tubabben ɗan ta’adda ne ya yarda da sulhun Gwamnatin Katsina, a wani gefen kuma sauran ƴan uwan shi da su ke ta’addanci tare su na ɗaukar shi a matsayin saniyar ware

An samu ruwayar cewa yarda da Sarki yayyi da sulhu ita ta tursasa shi gusawa zuwa ƙauyen Illela dan ya soma sabuwar rayuwa amman sauran yaran shi sun ka ƙi bin shi.

Sauran ƴan bindigar da Dan Da ya goranta gami da sa bakin gungun su Alhaji Dankarami sun kai hari yankin Illela, su kuma sun ka maido musu. Harin ya tilasta ma ɓangaren su Dankarami barin makaman da sun ka kai harin da su, harda wata bindiga ta kariya mai suna Anti-aircraft gun. Maharan sun samu tarin ganimar makamai. Wannan shi ya baƙanta ma ƴan wancan gungun rai kuma ba su yafe ba.

Wasu majiyoyi sun ce ƙaramin ƙanen Sarki an kashe shi, mai suna Chirwa, tareda matar shi inda wasu ukku kuma – Kabiru, Tanimu, Suleiman – sun ka jikkata, yanzu haka su na wata Asibiti a garin Katsina wajen neman magani.

Abubuwa sun taimaka wajen haddasa ƙyama da ƙiyayya tsakanin ƴan gungun biyu. An samu labarin cewa ƴan gungun Sarki su na hana wasu ƴan bindiga kai hari a yankin kuma su hana su kyayata bisashen su a wajen duk da dakwai tarin ciyawa a yankin.

Ta bakin wasu majiyoyii, Dankarami, Dangwate da Mai Komi sun kai harin ramuwar gayya dan su amso makamin su Bindigar Anti-aircraft, wanda an ka ce ya kai kimanin kudi Naira miliyan biyar (N5m).

An ce sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe 5 na yamma ranar Alhamis. Ta bakin mazamna yankin , sun kai wajen su ɗari ukku (300) kowanen su ɗauke da makami.

Majiyoyi sun ce da isar su, sun ka fara harbin kan mai uwa da wabi a ƙauyen, mutanen ba su sani cewa ƴan gungun Sarki su na sane da harin ba.

Wata majiya ta ce rashin jituwar saɓani ne tsakanin masu goyon bayan sulhu da waɗanda ba su yarda da shi ba. Amman duk da sulhun ba su hannanta makaman su hannun hukumomin tsaro na Gwamnatin Katsina ba.

Kenan abunda ya jawo gungun Dangwate yankin Illela shi ne dan su kama shugaban gungun. Da isowar su sun ka fara bincike gida-gida da zummar kama shi.

Da sun ka kawo ga gidan Sarkin Fawa Mu’azu, wanda shi ne shugaban mahauta a yankin, sun samu bindiga a gidan shi sai sun ka yi ƙiyasin ɗan sa kai ne, ɗaya daga cikin maƙiyan su kenan.

Ya nanata musu cewa shi ba ɗan sa kai ba ne, ana cikin haka sun ka harbe shi har lahira.

Majiyar ta ce maharan sun kai wajen sa’o’i takwas (8) su na ta’adi a ƙauyen, inda sun ka ƙone motoci da shaguna, sun ka kuma gudu da dukiya mai tarin yawa. Amman duk da ba su cike burin su na kama Mani ba wanda ya yarda da sulhu da Gwamnatin Katsina.

An ce sun sake komawa dajin inda sun ka gwabza da ƴan gungun su Dankarami, sun ka kashe da yawa daga cikin su. Mutane sun ce fiye da mutum ɗari (100) sun mutu, harda ƙananan yara.

Dankarami shi kan shi ya tsallake rijiya da baya saboda an harbe shi a hannun, inji wata majiya.

Hukumomin tsaro ba su kai musu ɗauki dan saboda faɗan na wa su wa su ne.
Madogara: DailyTrust

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post