Hannun ka mai sanda Malam Bahaushe – Ɗankasawa

Tun bayan yaƙin Danfodio na shekarar 1804 wanda wasu ke sanya ma rigar “Jahadi”, Hausawa da yawa sun rinƙa ɗaukar Fulani a matsayin yan uwa su, su kuma Fulanin (akasarin su ba dukkan su ba) su na kallon Hausawa ba su kai darajar shanun su ba. Yaƙin Danfodio dai marubuta tarihi na gida da na waje su na mishi kallon hadarin kaji saboda abubuwa da yawa, amman cikin waɗannan abubuwan mutane sun fi kafewa a waɗanga dalilai guda biyu, na farko cin amanar zamantakewa, na biyu fakewa da addini dan neman mulki. Wani Bahaushe manazarci mai suna Ɗankasawa Ɗanbaskore ya yi tsokaci gameda hare-haren ta’addancin da Fulani ke yi a Arewa inda har yayyi abunda Hausawa ke kira waiwaye adon tafiya – ya taɓo yaƙin Danfodio wanda ya wakana a ƙarni na sha-tara (19). Ba shi kaɗai ba, manazarta da yawa zancen da ke kan bakin su kenan a kullum sanadiyyar ta’addancin da Fulani Makyaya ke aikatawa a yankin Arewacin Nijeriyar. Su na ganin kamar kwatamkwacin abunda ya faru ɗaruruwan shekarun da sun ka gabata shi ne ya ke maimaita kan shi.

Ga cikakken bayanin na shi gamida gyaran GobirMob
Lokacin da yan ta’addan Fulani sun ka fara aiwatar da ta’addancin su a yankunan jahohin Arewa; Benue da Kudancin Kaduna, Hausawa da yawa sun ɗauka kamar guguwar ba za ta kawo gare su ba, su na ganin kamar Fulani na su ne. A yau ta’addancin da Fulani su ke yi a garuruwan Hausawa ya fi waɗanda sun ka yi a yankunan Jahar Benue da Kudancin Kaduna yawa.

Mutanen yankunan Benue da Kudancin Kaduna da Ƙasashen Yarabawa sun tashi tsaye wajen kare junan su daga hare-haren ta’addancin.

Amman duk da irin kisan kyasun da Fulani su ke yi ma Hausawa a jahohi irin su Sokoto da Zamfara da Katsina da Kudancin Kaduna, da sauran wasu jahohi ka taɓa jin inda mutanen sun ka samu damar fitowa su kare kan su ko kuma Sarakunan Ƙasar Hausa sun ka fito fili ƙarara sun yi Allah wadai da abunda ake yi musu? Ka taɓa jin kungiyar Miyetti Allah ta yi magana, ta ce ba daidai ba ne? Sai fa in an taɓa dangin su, Fulani!

Shekaran jiya ba’a yi ko sati biyu ba Yarabawan jahohin Ondo da Oyo sun ka ba Fulani Makyaya wa’adi su bar musu yankin su inda har abun ya zo da ɗan rikici. Sunday Igboho ya jagoranci matasa inda sun ka far ma maɓoyar su a wani dajin jahar, daga nan sun ka je gidan Sarkin Fulani sun ka ƙone mishi gida da motoci da kisan bisashe da mutane, sun ka ce su na zargin shi da goyon bayan ta’addanci a jahar. Saboda ko kuɗin fansa so tari fadar shi ake kaiwa ya kai ma ƴan uwan na shi kamin mutanen su samu kubuta.

Ƙungiyar Fulani Makyaya Miyetti Allah da wata ƙungiyar Arewa sun fito fili sun nuna ma Hausawa ɓangaranci, sun je har Ƙasar Yarabawa dan neman sulhu saboda wannan, inda su kuma Hausawa duk tsawon lokacin da an ka kwashe ana musu kisan ƙare dangi a jahohin Arewa-maso-yamma ba wata ƙungiyar da ta fito ƙarara ta ce abunda ake musu a bari. An yi walƙiya mun gan ta!

Hausawan Nijeriya marayu ne. Sarakunan su yawancin su Fulani ne. Malaman addinin su akasarin su Fulani ne. Uwa uba Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Ƙasa ma Bafulatani ne. Ku lura ko ƙungiya Hausawa sun ka yi a wani gari ko wata ƙasa, zaka ga Sarkin Hausawan Bafulatani ne, misali da Sarkin Hausawan Turai, kuma duk wanda ya san Fulani ya san su da ƙabilanci. In ku na shakkar ƙabilancin Fulani, ku tambayi waɗanda sun ka san su.

Hannun ka mai sanda Malam Bahaushe. Matuƙar Ƙasar Hausa ta cigaba da zama ƙarƙashin Sarakuna Fulani, to Fulani za su cigaba da cin amanar Hausawa. Ku tashi tsaye ku kare kan ku tunda kun ga abubuwan da ke faruwa da ku a yau.

Amfanin hankali aiki da shi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post