Hausawa kar ku bari Fulani su yaudare ku – Shawarar Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu, Shugaban ƙungiyar fafutukar kare martabar ƙabilar Igbo tareda kafa ƙasar Biafra wato Indigenous People of Biafra (IPOB) a yau Laraba ya sanarda cewa ƙungiyar su ba ta faɗa da mutan Hausa, ya ce faɗan su da Fulani makyaya ne, da su ke shiga gonakkin su, su na kashe musu ɗiya da mata tareda yi ma ƴanmatan su fyaɗe. Kanu ya ƙara da cewa ya na mutumta Hausawa sosai saboda mutanen kirki ne, masu son zaman lafiya.

Ya ce Hausawa mutanen arziki ne, dan saboda yardar da Ƙabilar Igbo sun ka yi da Hausawa har sun ka zaɓi Bahaushe magajin gari sau biyu (2) a Jahar Enugu.

Amman Fulani makyaya babu zancen zaman lafiya a duk inda su ke. Yanzu ta ya bayyana kashe-kashen da ke gudana a Arewa da Kudancin Nijeriya duk alhakin shi na kan su, ba su bar kowa ba.

A wata sanarwa da ya fitar wadda GobirMob ta fassara, Shugaban ya ce babu mamaki Fulani su ke saurin laɓewa ƙarƙashin Hausawa, su kira kan su Hausa Fulani. Yacce tun shekarar 2015 mutane ke jin miyagun abubuwan da Fulani ke aikatawa can da nan a Nijeriya. Da zarar sun tashi neman wurin malaɓa sai su kira kan su Hausa Fulani dan su cigaba da yaudarar mutane. Ya shawarci Hausawa cewa su bar yarda miyagu su na laɓewa ƙarƙashin su dan kar su shafa musu kashin kaji.

Mazi Nnamdi Kanu ya ce Ƙabilar Fulani yaƙi ne su ke kamar wanda Usman Danfodio yayyi na neman sarauta a Ƙasar Hausa, dan haka mutane su hankalta. Ya ce kowace ƙabila a Nijeriya ba su ɗauke ta bakin komi ba, a gurɓataccen tunani irin na su. A ƙarshe ya bayyana cewa mutane za su gode mishi da ya fara tona asirin su tun farko kafin kowa ya assaho. Sai yanda su ke bayyana halayen su na asali.

Ga ainahin sanarwar nan ku karanta:

No wonder they hastily resorted to mouthing their usual nonsensical Hausa-Fulani overnight. Since 2015 all we have been hearing is Fulani this Fulani that, but due to the heat coming from God’s chosen Children of Light (IPOB), they have resorted to their usual deceptive Hausa-Fulani combo in the hope of hiding under the usually civil and well behaved Hausa to evade the wrath of the people.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post