Jami'an Sojin Nijeriya sun ceto Mutane 3 da Mahara sun ka yi garkuwa da su a Nasarawa

Mun samu ruwayar cewa Dakarun Operation Whirl Stroke sun ceto mutane ukku da an ka yi garkuwa da su a Mararabar Udege da ke karamar Hukumar Nasarawa ta Jahar Nasarawa. Maigudanarwa kan ayyukan watsa labarai na tsaro, Major General John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa yau Juma’a, 8 ga watan Janairu.

Enenche ya ce an kashe ɗan ta’adda guda yayin musanyar wuta da ƴan bindigar wanda ya gudana a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa mutanen ukku da an ka kubtar tuni sun haɗu da dangin su.
Madogara: Hutudole

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post