Sojojin Nijeriya sun yi ba ta kashi da Ƴan Ta'adda; sun ƙwato shanu (Photos)

A daren jiya Juma’a 1 ga watan Janairu Ƴan Bindiga sun shiga har cikin garin Tarah da ke da nisan kilomita goma (10)
daga Sabon Birnin Gobir a babbar hanyar da ke zuwa Isa, a daren Yanta’addan sun yi nasarar korar shanu da dama zuwa hurumin garin Idi. Sojoji da mutanen garin na Tarah, garin Zago da wasu ƙauyukka sun bi Ƴanta’addan har cikin hurumin inda sun ka yi nasarar dawoda shanun na su gaba ɗaya.

Wata majiya ta tabbatarda cewa an yi musanyar wuta sosai tsakanin Sojojin Nijeriya (Nigerian Army) da Ƴanta’addan amman babu asarar rai har Yanta’addan sun ka gudu an ka samu nasarar dawoda shanun.

Jinjina ga rundunar Sojojin Nijeriya a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jahar Sokoto da sauran mutane da sun ka sadaukarda rayuwar su dan samun wannan nasara. Shekaran-jiya mun samu labarin cewa Ƴan Bindigan sun aiko saƙo cewa za su kawo hari da babura dubu ɗaya (1,000) a yankin.

Kamannai daga Garin Tarah Sokoto:

Dakarun Soji bayan ba ta kashin.

Dakarun Sojin Nijeriya sun yi nasarar ƙwato shanun mutanen Tarah.

Shanun da Dakarun Sojin Nijeriya sun ka ƙwato.
Madogara: Lawali Kakale Gobir

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post