Tabbas Bahaushen mutum ba ya da Ƙabilanci – Ɗankasawa

Duk wanda ya san Bahaushe, idan zai faɗi gaskiya tsakanin shi da Allah, ya san Bahaushe ba ya da ƙabilanci.

Wannan shi ne dalilin da ya sa a duk faɗin duniya babu wata ƙabilar da ke da kalmar da ta ke kiran na cikin ta da ita dan kawai ba ya musulumci sai Hausa. Hausawa ke da kalmar “Maguzawa” da ke nufin Bahaushen da guje ma tafarkin Musulumci.

Rashin ƙabilancin Bahaushen mutum yassa ya goyi bayan Usman Danfodiyo, har ya yi ma sarakunan ƙasar shi, jinsin shi, tawaye. Bahaushe bai cika tarayya da Maguzawa ba duk da ƙabilar su ɗaya dan kawai Bamaguje ya guje ma addinin Musulumci.

Ka duba da kyau ka gani, Bahaushe ba ya da ƙungiya ta addini ko siyasa ko sana’a wadda ya keɓe ta ga Hausawa kawai. Saɓanin wasu ƙabilu. In dakwai kuma a gaya muna mu ji.

In siyasa ta taso, Bahaushe ba ya cewa sai na shi zai zaba. Wannan shi ya sa ko a ƙananan hukumomi da jajohi da ƙasashen da Hausawa ke da gagarumin rinjaye da wuya ka ji sun zaɓi Bahaushe. Su dai in kai Musulmi ne, na su ne kai. Bahaushe namijin duniya – kowa na ka!

Bahaushe zai ba ka auren diyar shi ba tare da ya kula da ƙabilar ka ba, matuƙar ya gamsu da musulumcin ka.

Amman sarakunan da ke mulki a Arewacin Nijeriya a yau sun ci amanar Hausawa. Su na sarauta a karagun sarautar Hausa, su na kwana gidajen sarautar da sarakunan Hausa na asali sun ka gina, su na magana cikin harshen Hausa, amman kullum so su ke su nuna ma duniya cewa su masu daraja ne dan su na Fulani. Shugaban da ya san ciwon kan shi ya kuma san ya kamata, ba ya nuna ɓangaranci a abubuwa.

Bari in ba ku misali.

Dubi darajar da ake kallon kujerar Masarautar Sokoto da ita – Sarkin Musulmi, magajin Malam Usman Danfodiyo da Muhammadu Bello, jagoran musulumci a Nijeriya gaba ɗaya. Amman kuma wai shi ne uban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta ƙasa. Saboda kasancewar shi uban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah shi yassa da matsalar ta’addancin Fulanin daji ta ke addabar yankunan Hausawa ta ta’azzara, maimakon ya fito fili ƙarara ya yi Allah waddai da waɗannan miyagun, sai ya toge ya na cewa wai ba Fulani kaɗai ba ne ƴan ta’adda.

Dubi yanda da ƙarfi da yaji sarakunan ƙasar Hausa sun ka tashi daga matsayin Amirai (jam’i na Amir) watau jagororin musulmi da Malam Usman Danfodiyo ya ba su tuta bayan yaƙin neman sarauta, sun ka koma Sarakunan Ƙasa, yanzu kuma su ke kiran kan su da Sarakuna Fulani. Sai ka ji mutum, irin tsigaggen Sarkin Kano Sanusi na biyu, wanda in ya na magana da harshen Hausa za ka ji ya na maƙewa da shaƙe murya kamar wata tsohuwar baturiya na koyon Hausa, na bugun ƙirji da ɗaga kafaɗa wai shi ga Bafulatani mai sarauta a ƙasar Hausa!

Bahaushe ba ya da ƙabilanci. Rashin ƙabilancin Bahaushe shi yassa an ka maida shi sakarai shawaraki. In kau rashin ƙabilanci ne ke sa ana yi ma Bahaushe kallon dolo, ya zama tilas ya tashi tsaye ya nuna ma duniya cewa shi fa ba dolo ba ne.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post