Yau Sarkin Gobir Tudu Madawa ke Bikin cika shekara goma (10) bisa Karagar Sarauta

A rana irin ta yau, 15 ga watan Janairu, Maimartaba Sarkin Gobir Toudou Madaoua ya hau karagar Masarautar Gobirawan Tudu, ɗaya daga Masarautun Jahar Tahoua. Sarkin ya hau karagar ne a shekarar dubu biyu da goma sha-ɗaya (2011) bayan rasuwar Margyayi Sarki Aboubakar Kadri Tawaye wanda yayyi yayi tun daga shekarar 1981 zuwa 2010.

An haifi Maimartaba Mahamadou Manirou Magagi Rogo a ranar 2 ga watan Yuni, a shekarar 1967 cikin garin Madaoua. Ya yi karatun matakin farko da na sakandare (CEG) cikin Madaoua, sannan ya yi karatun Ƙereƙere (Engineering) a Ƙasar Nijeriya. Ya yi aiki tareda Ma’aikatar tace iskan gas ta Jahar Tillabery (Tillabery Regional Hydraulic Depertment), Ma’aikatar tace iskan gas ta ƙasa (Niger Ministry of Hydraulic) da sauran ayukkan gwamnati da dama.

Bayan rasuwar Margyayin Sarki, Elhj Aboubacar Kadri Tawaye a shekarar 2010, Maimartaba Mahamadou Manirou Magagi Rogo ya hau karagar Masarautar Gobir Tudu Madawa a shekarar dubu biyu da sha-ɗaya (2011). Ubangiji Allah ya taya ka riƙon. Ameen.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post