Asirin Ƴan Ta'addan Fulani ya tonu, an gano Matan su ke kai musu ƙwayoyi

Yau dai Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jahar Sokoto ya fasa ƙwai. Mun karanta a jaridar DailyTrust, ya ce sun gano cewa Fulanin nan ƴan ta’adda da ke yawan kai hare-hare a garuruwan Arewa-maso-yamma, su na kashe bayun Allah, su na sacewa tareda ƙone dukiyoyin su, yanzu ta tabbata su na sha tareda tu’ammali da muggan ƙwayoyi. Kuma matan Fulani masu tallar nono a cikin ƙauyukka da garuruwa, su ne ke sayowa su na kai ma mazan na su a cikin daji.

Saboda haka mu na kira ga hukumar yan sanda da hukumar yaƙi da tu’ammali da muggan kwayoyi watau NDLEA su fara tsarewa su na binciken matan Fulani masu tallar nono.

Wata majiya ta tabbatar muna cewa wasu cikin matan Fulani da ke tallar nono na kai ma mazajen su yan ta’adda diddigi da bayanan sirri gameda hali da shirin da mutanen cikin gari ke ciki, watau su na yi ma mazan su leƙen asiri.

Ba mu ce a ƙaurace ma hajar da matan Fulani ke saidawa ba, amman mu na kira da babbar murya ga mutane da su yi hattara dan gudun kar a rufe ƙofa da ɓarawo.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post