Yaƙi da Ƴan Ta'adda shi ne mafita ba Sulhu ba – El-rufai

Gwamnan Kaduna, Nasir El-rufai ya ce yaƙi da bakin bindiga shi za kawo ƙarshen Ta’addanci a Arewa

Gwamna Nasiru Ahmed El-rufai, gwamnan jahar Kaduna, ya ce rashin haɗin kai tsakanin gwamnonin yankin Arewa-maso-yamma na ɗaya daga cikin abubuwan da sun ka hana shawo kan matsalar ƴan fashi masu garkuwa da mutane.

A hirar shi da BBC, gwamnan ya ce ya na da ra’ayin a buɗe ma ƴan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatin shi da masu garkuwa da mutane.

“Idan Gwamnatin Tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na ƙasa ba, an shiga dazukkan nan an kashe ƴan ta’addan nan a lokaci ɗaya, to za mu cigaba da zama cikin matsala,” in ji gwamnan.

A cewar shi: “Mu a Kaduna mu na haɗa kai da Jahar Niger. Gwamnan jahar na kira lokaci zuwa lokaci mu na hada bayanai. Mu na abubuwa tare da su.”

Ya bayyana hakan ne a yayin da ƴan bindigar ke cigaba da cin karen su babu babbaka a yankin na Arewa-maso-yamma.

Hakazalika, kalamin na shi ya sha bamban da na wasu gwamnonin yankin waɗanda ke ganin yin sulhu da ƴan bindigar shi ne mafita ga rashin tsaron da ke addabar Arewa-maso-yammacin Nijeriyar.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post